Idan ba ke complete hausa novel document

Idan ba ke complete hausa novel document

IDAN BA KE!!! Complete Hausa Novel Written By Na'ima Sarauta



Posted byAi Hausa Novel
Price₦500
CategoryHausa Ebooks
Uploaded On6 Jan, 2023
Upload Time8:29 pm
Hits218 Views
Author

Writer Group

Novel Genre

CommentNo Comments


Gudu Saniyar take tana bin ta a baya itama, hannunta riƙe da sanda na korar Nagge, tamkar wanda suke wasan tsere haka Saniyar ke gudu a cikin jejin ita ma bata fasa bin ta ba, sauran Naggen suna gefe guda ko wacce na cin ciyayi wanda bisa kuskure tana can tana bin Saniya ɗaya tilo, sauran Naggen suka faɗa  cikin gonar wani manomi, a yunwace suka rufarwa albarkatun gonar. Cikin siririyar muryarta mai nuni da Yarintar ta, da kuma nuna cewa ita  ɗin zallar bafullatanar Yola ce ƴar Usul. "Waru! Waru! Waru" shi ne abin da yarinyar ke ta nanatawa cikin hausarta ta Fulani, yayinda Saniyar tuni tai mata nisa cikin gajiya wa da bin Saniyar ta tsaya a wajan wata gaɓar ruwa tana riƙe ƙugunta ta ce "Bone, lalashewa ta samu Nagge Aradu"  da sauri kuma ta ɗauki sandar tana ƙara yin kan Saniyar ganin ta tsaya da gudun da take, cikin sa'a ta cimmata tana zuwa ta kama ƙahonta tare da ƙifƙifta idanunta alamar zallar fitsarar dake tattare da ita "d'ume ngid'd'a?" Ma'ana "me kake so?" Kallon ta Saniyar ta yi sai kuma ta kaɗa jela tare da zubewa a wajan ta shiga shura ƙafafuwa kamar zata mutu, cikin tsoro haɗi da razani HALISA ta ce "Jomirawo ka taimakeni" ta faɗa tana kallon Saniyar wacce tai male-male a ƙasa ga wani ruwa mai kama da jini na fitowa ta ƙasanta, kuka Halisa ta sanya domin idan Saniyar ta mutu a nan wajan ta shiga uku, itama watan mutuwarta ya kama. Tsayar da kukan tai kafin ta fara duba cikin jeji babu kowa sai ita, ga wani kwantaccen baƙin hadari dake ƙasa wanda a koda yaushe zai iya tashi.


Juyawa tayi ta nufi wajan wata bishiya inda ta hangi ƙaramar igiya a jiki, tana zuwa jikin bishiyar ta zame hular Fulanin dake kanta, nan da nan sumar kanta ta sauka wacce take jajir babu alamar baƙi ko ɗaya, gashin ba wani cika ne dashi ba, kawai tsayin gashi gareta, domin har fatar tsakiyar kanta ana iya ganowa. cikin sayin jikinta ta fara jan igiyar  tana ƙoƙarin kunce igiyar gaba ɗaya daga jikin reshen bishiyar, kamar daga sama taji saukar wani abu mai sanyin gaske zuwa kafaɗunta. Cak ta tsaya tana sauraren yadda abin ke tafiya sululuuuu a jikinta har ya gama sauka, hannunta ta miƙa da nufin kama abin da ya sakko mata domin bata da tsoro ko kaɗan, cikin rashin sa'a hannunta ya sauka saman ƙaton kan maciji wanda yake kwance a jikinta, wani santsi-santsi ta ji a jikin macijin ga wani sanyi sosai dake ratsa fatar jikinta, bata gama yadda da abin da zuciyarta ke ayyana mata ba, a hankali ta juya wani ihu ta kurma wanda ya yi daidai da ɗaukewar numfashinta, baya tayi zata faɗi kafin ta kai zuwa ƙasa macijin ya yi wata girgiza cikin sakanni ya juye zuwa wani saurayi wanda jikinsa ya ke sanye da wasu haɗaɗɗun kayan sarauta na farin saƙi, fari ne tas amma kamar Fatar mace haka fatar hannunsa da sauran jikinsa suke gaba ɗaya gashi ya kwanta luff. Zubewa ya yi a ƙasa ta faɗo jikinsa idanunsa a kan fuskarta, ya jima yana kallonta kafin cikin izza da nutsuwa ya ce "kin tsoratani, kin tsorata kanki Danejo, banyi niyyar zuwar maki ba yanzu" Danejo sunan da ƴan rugar Rome suke faɗawa Halisa ke nan. Sai da ya gama Kallon ta sosai, kallon da ya jima bai mata ba tun tana zanin goyo matsayin Jaririya. Ɗaukanta ya yi ya nufi inda Naggen suke yana zuwa ya tarar da wannan Saniyar dake Shure Shure ta haihu, ashe daman ciwon haihuwa ke damunta.  Halisa ya kalla yana sakin Murmushi kafin ya zaro harshesa waje sai ga wani zobe ya bayyana, cikin sauri ya saka mata zoben mai ɗauke da tambarin wata masarauta, kafin ya yi Girgiza sai ga shi ya sauya kama, kamarsa a fuska na nan, amma kayan jikinsa sun sauya sun koma irin kayan Fulani sak komai da komai, goya Danejo ya yi a bayansa, ya ɗauki jaririn Saniyar cikin nutsuwa ya fara kaɗa Naggen zuwa Rugar Rome. Kamar ƙifatawar idanu haka ya ƙaraso Rugar.

Iskar dake kaɗawa na alamar tashin hadarin ya sanya matashin ɗaga kansa sama, yana kallon yadda gajimare ke haɗa kansa. A nutse kuma ya fara bin Rugar Rome da kallo ba wata babba  bace, amma Ubangiji ya albarkaci rugar da dabbobi musamman Nagge, gasu manyan gwanin sha'awa yawancinsu jajaye ne kafin ka samu farar saniya zaka daɗe. Wasu sun dawo daka kiwo wasu kuma na hanya sbd rashin yawaitar mutane da babu a rugar, daidai wajan wata bukka ya Ƙarasa yana gyara riƙon da ya yi wa Jaririyar Saniyar kafin ya ce "Sannunmu dai" ya faɗa a taushashe jin shiru ya sanya ya ƙara buɗe muryarsa mai sanyi ya ce  "Afuwanku dai" daga cikin bukkar wata ƙaramar murya ta amsa da faɗin "Waye nan?" Ta faɗi hakan tana fitowa, lokacin da Idanunta ya sauka acikin ƙwayar matashin gabanta taji ya faɗi saboda yadda taga ƙwayar idanunsa, gane cewa kamar ta tsorata da yanayinsa ya sanya ya lumshe idanunsa kaɗan tare da buɗewa ya ce "Ga ɗan uwanki na kawo shi, arado bashi da lafiya ne can na ganosa yashe a jeji ba rai, har naggenku ya samu zuri'a" yana faɗin hakan ya ajjiye Jaririyar Saniyar a ƙasa wacce take jajir da ita Kuma ƙatuwa. Shatu dai binsa take da Idanunta domin bata taɓa ganin mai kama dashi a rugar ba sai yau, kallon da yaga yai yawa ne yasa ya ce "Shai a mata magani" a hankali ya sauke Halisa Dajeno ya kwantar a ƙasa a nan gaban bukkar kamar zai juya ya tafi sai kuma ya ƙurawa zoben hannunta idanu wanda yake sheƙi sosai ga tambarin masarauta nan ya fito sosai a jikinsa, a ransa yake ji kamar bai dace daya mallaka mata wannan zoben ba, amma bashi da wani zaɓi dole ya bata ta haka ne kawai zai lalubota a duk sanda ta ɓace masa, tun tana ciki yake fama da rainonta lokacin haihuwarta ne kawai bai sani ba.

Ba tare da ya ƙara cewa komai ba ya juya da sauri ya fara tafiya tare da shankwana, yana barin wajan ya ƙara yin girgiza wata iska mai daɗi da guguwa ta mamaye gaba ɗaya cikin Rugar Rome. Nan take ya koma asalin macijinsa kamar yadda ya bayyana a farko, yana iya komawa duk suffar da yaga dama cikin ƙaramin lokaci amma zama maciji yafi masa daɗi sbd yawaitar macije dake cikin jejin daya zagaye Rugar Rome, a haka ya sulale tare da komawa cikin jejin...


Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.

Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com


Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

 



Author’s Contact

  • Name : Na'ima Shu'aibu Sulaiman
  • Wattpad Handle : @Nimcy Sarauta
  • Nick Name : Nimcy Sarauta
  • Whatsapp Number : 08119237616
  • Nationality : Nigeria
  • Group : Elegant Writers Association

The Book is not free


Post a Comment

0 Comments

Ads


Click Here To Download This Book