Mayraah Page 10 Complete Novel By Khaleesat Haiydar

Mayraah Page 10 Complete Novel By Khaleesat Haiydar

 💖💖 *MAYRAAH*💖💖



_By Khaleesat Haiydar_✍🏻


10.....


Mikewa Musharraf yayi ya amshi Envelope din hannun Mami ya dake yace "What is it for?" Mami tace "Ka duba" Tana fadin haka ta zauna saman kujera tana kallonsa, a hankali ya ciro takardan cikin Envelope din ya warware yana karanta rubutun jiki, same content ne da wancan da aka fara kawowa, sai dai wnn an kara abubuwan da suka linka na farkon tsayawa a rai, Musharraf ya kalli Mami dake ta kallonsa babu ko kiftawa, zaunawa yayi side dinta yayi kasa da murya yace "And did you believe this Mami?? ke kin yarda da wannan takardar?" Mami dai kallonsa kawai take, can tace "Uhnn abun ne ai da mamaki da daure kai" Musharraf ya mike a fusace yace "Mami i swear to God wannan ba komai bane facce sharri, karya da hassada, daga ganin wannan rubutun kasan mahassadi ne yayi sa, beside dama ai babu wani auren da baya zuwa da kalubale barin idan shaidanu suka cika lamarin from every angle, all i know is that, koma wani mara aikin yi ne ya turo da wannan saƙon to yayi a banza, babu abinda hakan zai canza...." A hankali Mami tace "Musharraf" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, Mami tace "Akwai abubuwan dubawa a lamarin nan...." Da mugun mamaki yace "Mami so u believe all this?" Mami ta girgiza kai tace "No ba wai nace maka na yarda bane my dear, kawai dai ina gudun abinda zai je ya dawo ne, this isn't a minor issue, sannan babu wasa a zancen aure don abu ne da ake son ayi sa na har abada...." Bai kuma ce mata komai ba ya bar parlon kamar zai tashi sama ya wuce dakinsa Mami ta bi sa da kallo, mikewa Mami tayi ta bi bayansa, bayan ta shiga dakin nasa tana kallonsa tace "Look Musharraf, bana son ka daga hankalinka, pray hard about it, Allah Ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairi, and i pray this should be between me and you, ba sai kace ma kowa komai ba, Allah ya daura mu kan makiyanmu, no need to disturb ur self, i gat ur back" Musharraf ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dama yasan Maminsa bazata taɓa juya masa baya ba, duk abinda yace mata ba haka bane, ita ma a hakan zata tafi a ba hakan bane, bata son komai yayi stressing din mata son dinta, because she loves him so dearly, he always reminds her of her late husband, shi yasa take jin sa har cikin ranta, and she can go any extent for him, mikewa Musharraf yayi ya kamo hannunta yace "Thank you for always believing in me Mami, and i appreciate ur support always" Ta sakar masa murmushi tace "Anything for you sweetheart" 

Ammi ce zaune dakinta sai Aunty Mariya da har a sannan ta kasa daina hawaye da ta tuna a hannunta zinarin nan yake aka sace sai ta kara rushewa da kuka, Maheer ma na tsaye dakin ya ma rasa abinda zai ce bayan Ammi ta kirasa ta gaya masa abinda ke faruwa, Ammi ta kalli Aunty Mariya tace "Wai baza ki rabani da wannan kukan da kike ba Mariya?" Aunty Mariya ta kara fashewa da kuka tace "Dole inyi kuka Ammi, ni fa aka ba abun nan a hannuna, kowa yasan ni aka ba ajiya, yanzu ta ina zan fara fisabilillahi? Waye yayi mana wannan aika aikan? sarkan kusan miliyan biyar, na shiga uku na lalace" Maheer yace "Yaushe Badiyya ta bar gidan nan?" Duk suka daga kai suna kallonsa, Aunty Mariya tace "Babu wanda tayi ma sallama kawai nemanta aka yi ko sama ko kasa" Maheer yace "To ita ta dauka" Ammi ta zaro ido tare da dafa kirji tace "Ka rufa mana asiri kada Hajja ta tsine mana Maheer, ta yaya zaka ce Badiyya ce ta dau zinari?" Aunty Mariya tayi shiru tana nazarin abinda Maheer yace, dazu fa da Hajja ta Kirata tana mata maganar zinarin Badiyya na zaune parlon, daga ita sai Hajja a parlor, kuma throughout today babu baƙin da suka hau sama banda Mama Ladi, Aunty Mariya ta mike tace "Wallahi babu tantama ita ce, don babu wani visitor da ya haura sama duk yau, Mama Ladi kuwa ko motsawa bata yi daga dakin Mayraah ba har yanzu" Aunty Mariya ta figi Hijab din Ammi zata fita, Ammi ta rikota tace "So ku ke ku jawo mana tashin hankalin da bashi da ranan karewa ne Mariya? Ta yaya za ace Badiyya ce ta dau zinari bayan ba ita kadai bane a gidan nan?" Maheer ya kalli Aunty Mariya yace "Ai kin ji irinta, ban san me yasa Ammi take haka ba, kuma wllh yanzu zan tafi gidan Hajjan duk inda Badiyya ta kai zinarin nan sai ta fito da shi wallahi idan ba haka ba in kakkarya yar iska" Aunty Mariya dake huci tace "Tare za mu tafi Maheer, sai dai duk abinda zai faru ya faru yau, idan ba tasan ta aikata rashin gaskiya ba ta yaya zata sidade ta gudu ta bar gidan ba wanda ya sani, yarinya shaidaniya kawai bayan gulma da munafurci ashe har da halin bera duk tana yi?" Ammi da hankalinta yayi mugun tashi ta fashe da kuka tace "Ni dai duk wanda ya fita da sunan zuwa gidan Hajja ya samu Badiyya da zancen zinari ban yafe ba koma waye" Daga Maheer har Aunty Mariya haka suka tsaya kallonta, Maheer yace "Toh Allah ya baki hakuri Ammi, yanzu dai gold din nan zai yi miliyan 5 ko ma fin haka, kuma babu ta yanda za a kai Mayraah gidan mijinta babu wannan gold din tunda su suka saka a lefe, don haka sai a san yanda za ayi" Ammi na goge hawayenta tace "Ba komai, ai anyi hotonsa a waya, Zan sa a shiga kasuwa a duba min sak irinsa, Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" Maheer ya juya ya fice daga dakin, Aunty Mariya ta bi bayansa. Aunty Mariya ta bi Maheer har zuwa dakinsa ta kulle kofar, a fusace Maheer yace "Kinga exactly abinda kika gani yanzu Aunty? To kullum a haka ake, kwata kwata Ammi bata son ace Badiyya tayi laifi balle a hukuntata, idan kayi magana tace bata son Hajja ta kullaceta ne saboda wasu dalilan da ta bar ma kanta sani, Hajja bata da aiki sai lakaba ma Badiyya maraici wanda wannan mentality din ya riga ya makale a kwakwalwar yarinyar yanzu, an lalata mata rayuwa kawai, babu wanda ya isa ya hanata ko ya sa ta, iskancinta take zubawa yanda ta ga dama...." Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa tace "Ai kaga Malam Bahaushe sai Allah kawai, da mutum ya rasa iyayensa ko makamancin haka sai ayi ta binsa da wai maraya ne shi, wanda wnn kalmar ba karamin tasiri yake a zuciyar yaron ba, yayi ta amfani da shi yana iskancin da ya ga dama, dama shi Maraya saboda iyayensa sun mutu sai aka ce a sangartasa har a bar sa ya lalace?" Maheer ya zauna gefen gado yace "Toh baki samu labari bane kwanaki har cewa tayi ita idan ba lecturer din da ke neman Mayraah ba to ita fa sai dai ta mutu, tayi ta iskanci iri iri a period din Ammi da Hajja na biye mata, infact i am fed up with all this wllh, har bana son a nuna Badiyya a kirata da er uwata saboda mugun halinta da yayi tsamari, yanzu ai ya ci ace tana da tsayayye ita ma tayi auren nan, amma babu ko daya, kullum sai dai wannan ya zo ya dauketa a mota ya dawo da ita, wancan ma ya zo ya dauketa ya dawo da ita a gidan Hajja, kuma Hajja bata da bakin magana don rufeta da fada take kamar zata mata duka" Aunty Mariya tace "Yanzu dai ba Ammi tace taji ta gani kar a ma Badiyya magana ba ita zata siyo wani gwal din? To ai shikenan, ko ba komai ni dai hankalina ya kwanta" Tana kai wa nan ta fice daga dakin.... 

Haseenah ta rike haɓa tana kallon Badiyya tace "Yanzu ke baki ji tsoron wannan abun da kika aikata ba Badiyya? Kilan ba ana can gida ya hautsine ana neman zinarin nan" Badiyya tayi wani dariya hade da taɓe baki tace "Kuma babu wanda ya isa yace ni ne don Hajja kadai ta ishesu wllh" Haseenah tace "Gold din nan fa zai yi miliyan hudu kila Badiyya" Badiyya ta hade rai tace "Ni dai in zaki hada ni da masu siyar da Gold da kika sani a kasuwa ki hadani in kai abun nan su bani kudina, waye zai san na sata ne gwal din idan ba fada aka yi ba tunda dai ba waya bace balle ace za ayi tracking, kawai ce masu zaki yi Mummynki zata siyar amma reciept ya ɓata tunda kince sun saba ciniki da ke" Haseenah tace "Ai ni tsoron abinda zai je ya dawo nake Badiyya, what if daga karshe suka gano na sata ne in one way or the other kuma gashi nayi involving Mummy a ciki, kin fa san halinta" Badiyya tace "Wallahi ke shegiyar matsoraciya ce Haseenah, babu wanda zai tsaya wani bibiyan zinari, abun nan fa family issue ne su kansu baza su so ya fita waje ba, kuma Hajja bazata bada chance din da kowa zai zargeni ba, haba sai kace baki san Hajja ba" Haseenah tace "To nawa zaki bani a ciki yanzu don nasan halinki da kudi, dama in bai min ba to wllh bazan yi hanyar siyarwa ba" Badiyya ta gyara zama tace "Ai wllh kin fi ni son kudi Haseenah nawa ne kawai ya fito fili, yanzu dai in sun siya miliyan hudun da kike ta cewa zan baki 500k a ciki" Haseenah tace "Kan uban can, to ai ni ba er iska bace, ungo abinki kije ki siyar da kanki" Badiyya ta mata wani kallo, can ta kyabe baki tace "To naji zan baki 1M in dai miliyan hudun aka siya, in basu siya haka ba to wllh bazan baki haka ba, ai ba wani ya sato min ba" Haseenah tace "Za ma su siya hakan, wnn fa da kyar in bai yi gram 45 zuwa hamsin ba" Badiyya dai sai murmushi take, Haseenah tace "To wai yanzu kina nufin kin hakura Mayraah ta auri Lecturer din naku tunda kin tsira da gold?" Badiyya ta mata wani kallo tace "Na hakura?? Ashe ban cika Badiyyar ba kenan, wllh Haseenah in kika ga anyi auren nan to faduwa nayi na mutu murus, amma ina me tabbatar maki baza ayi auren nan da Mayraah ba matsawar in numfashi, ba boka ba Malam" Haseenah tace "To sai da ke za ayi auren kenan?" Badiyya tace "Aa ban ce da ni za ayi ba, ba sai an samu an lalata auren ba kafin in cusa kaina? Ai yanzu lalata auren shine babban aiki tukun... Akwai maganganu da yawa da nake son in gaya maki amma sai bayan naga an fasa auren don bana son soyayya dadi ya kwashe ki kije ki gaya ma Maheer ba tare da kinsan kin yi ba" Tana kai wa nan ta mike tace "Kin ga akwai wani gida da muke son zuwa yau din nan, mun fi sati muna kokarin gano gidan sai dazun nan da safe Allah ya sa aka gano, Haseenah tace "Wani gida kenan?" Badiyya tayi wani murmushi tace "Duk za a baki labari kwantar da hankalinki kawata, gidan ma ba daya bane ba biyu, gidaje kusan hudu ne, wallahi na kashe yafi dubu dari biyu wajen neman gidajen nan, yanzu haka bani da ko sisi a account dina, shi yasa nayi mugun farin ciki da samun gwal din nan" Haseenah na jijjiga kai tace "Baddieeeee" Badiyya ta wani juya tana dariya tana kas kas da chewing gum tace "Say it louder" Haseenah tace "Ai baki sani ba, ko da ace baki samo gold din nan ba na shirya daga dubu dari zuwa sama in baki contribution in dai akan ki lalata auren Mayraah ce, i will support u 100%, baki ga kullum follow up nake kan issue din nan ba, ai ba kiran banza nake maki ba kullum inji yanda ake ciki, A whole me fa Haseenah yarinyar da a haihuwan kaji na haifeta tayi ma walakanci of the highest order a gidansu daga wai an kai ni in gaida uwarta, ai har yau da wannan abun nake kwana nake tashi yayi min mugun ciwo wllh, sannan har Maheer zai iya daukan gaba da ni a kanta for days, Wallahi ko da wasa bayan aurenmu da Maheer wataran ta shirya tace ta zo wajen yayanta sai na mata abinda har ta koma ga Allah bazata manta ba kuma a gaban yayan nata, babu kuma abinda ya isa yayi wllh" Badiyya tace "Ke naki duk me sauki ne Haseenah, bari in je Baddo na ta jirana tun dazu, duk yanda ku ka yi da masu siyar da gold din ki kirani ki gaya min" Haseenah tace "In sha Allahu" Daga haka Badiyya ta fice daga dakin Haseenah, mayafi babba ta yafa yau gudun fadan Maman Haseenah don matar ta fiye takura a cewarta.

Yau Wednesday Mayraah na class suna rubuta test din wani lecturer dinsu, invigilators sun kusa hudu a ajin suna invigilating dinsu, suna shiga da some minutes Mayraah ta gama answering questions dinta duk da mugun wahalan da question din suka yi, Badiyya na class din sai satan amsa take a tsorace ta cikin wayarta da ta cusa a cinyarta, kamar daga sama taji ance "Stand up" duk ta gigice har sai da wayar ya fadi kowa ya juya yana kallonta with shock a class din, lecturer din da ya kamata ya duka ya dau wayar sannan ya kwashe script dinta yace "Get out" Juyawa tayi da sauri ta fice daga class din duk aka bi ta da kallo, Lecturer din yace "You will come back for this course in sha Allah, so let me see weda u will have another partner" Masu kokarin satan amsa dama duk suka shiga taitayinsu aka yi jigum, lokacin submitting nayi Mayraah ta mike ta taje ta yi submit din nata sannan ta fita daga class din, fita tayi outside the department don taga ko Dr Musharraf ya zo makarantar amma bata ga Motarsa a parking space ba duk da tasan monday da Tuesday kadai yake zuwa kuma week din nan duk bai zo ba, gashi basa wani magana sosai a waya yanzu, yawanci ma a kashe zaka ji wayarsa wani lokacin, sai in ya kunna ne yake kiranta suyi few minutes su a magana kuma shikenan, wanda hakan na damunta sosai, in just 2 days time bikinsu, kuma daga yau bazata sake shigowa department ba sai bayan bikin, duk da suna da test har biyu on friday amma duk lecturers din sun daga mata kafa za su bata make up test idan tayi resuming, dama iya test din yau ne ya kawota makarantar, don haka ko su Hamida bata tsaya yi ma sallama ba ta nufi gate din makarantar don samun adaidaita sahu a waje ta wuce gida za ayi mata gyaran jiki.... 

Mami ta sakko downstairs jin hayaniyar da ya cika parlor alhalin ita dai tasan daga ita sai mai aikinta ne a gidan, da mamaki take bin su Hajiya Halima da Mama Harira da kallo, yau har da matar yayan Abbansu Musharraf da bata ko zuwa gidan don banda ita ma aka kai lefe, Mami tace "Lafiya menene yake faruwa haka?" 

Continue making ur payment before the end of free pages 

07087865788✍🏻

WhatsApp only


Mayraah Page 11 By Khalesat Haiydar


Post a Comment

0 Comments

Ads


Click Here To Download This Book