Page 12
Hajja na shigowa Bedroom din Ammi ta rafka salati ta fashe da kuka a rikice ta zauna kasan carpet tace "Allah mun gode maka da wannan jarabawar" Mama Ladi da tuni tayi cilli da gyalen da ta yafa tace "Toh wai na taɓa jin inda aka fasa aure babu wani dalili ni Ladiyo? Kamata yayi ai a turkesu su fada mana uwar me aka masu za su fasa aure, ko kuma kawai a kai su caji ofis a bi mana hakkinmu, da wani ido za mu kalli jama'an da muka tara?? Ko dai yan iska ne yaron da iyayensa? A kira mana Meran mu ji ko wani sa'insa ya hadasu da yaron ne, ko kuma a kai ni gidan ni inji dalilin fasa auren" Ammi dai tayi nisa tunanin da take don tayi kukan har ta gode Allah, wai a haka ma fa bata san dalilin fasa auren ba ina ga ta sani, Aunty Mariya dama bata bi su Hajja zuwa dakin Ammi ba don ganin yayarta cikin kuka na kara karyar mata da zuciya, Abba kawai take son gani don gaya masa kar ya sanar ma Ammi dalilin fasa auren nan for her mental health, gun Maheer dake zaune parking space ta tafi, he looks so heartbroken and sad, Aunty Mariya ta fi minti biyu tsaye amma ta ma rasa abinda zata ce masa kamar yanda shi ma bai ce mata komai ba kansa a sunkuye, parlon baƙi ta nufa daga karshe duk jikinta a sanyaye, tana sallama kuwa ta tadda Abba har sannan a ciki, shi kansa kana ganinsa kasan ya shiga damuwa ba kadan ba, Aunty Mariya ta zauna saman kujera nan da nan hawaye ya cika idonta tace "Alhaji ina ga da an boye ma Ammi dalilin fasa auren nan because of her health, kar a gaya mata don Allah" tana fadin haka ta fashe da kuka, Abba dai yayi shiru yana kallonta ya kasa cewa komai, bayan few minutes Abba yace "Ina Mayraah?" Aunty Mariya ta buda ido sosai, infact duk wannan abinda ake babu ma wanda yaje ya ga halin da yarinyar ke ciki, Aunty Mariya tayi karfin halin cewa "To Allah ya sa yaron bai gaya mata ba dai, i think tana dakinta tare da kawayenta" a hankali Abba yace "Ki dubo min ita" Mikewa Maheer yayi yana kallon Hamidah da ta nufo parking space din da yake zaune, tun bata karaso ba yace "Where is she?" Hamidah tace "Wallahi na duba upstairs gaba daya bata nan, har dakin dake downstairs she is not inside" Maheer ya buda ido yace "What?" Barin ta yayi wajen a tsaye ya nufi cikin gidan da sauri. Hankali tashe Maheer ke searching all of the house for Mayraah, har kiran wayarta yayi yaji switch off, Aunty Mariya da ta shigo ita ma a lokacin duk ta gigice bayan Hamidah tace mata ai Mayraah ce bata gidan, ita dai Hamidah was so confuse at this time don bata san abinda ke faruwa a gidan ba, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo, babu fuskan wanda ya kalla ya wuce sama direct, Maheer ya bi bayansa yace "Wait, we can't find her in this house, she is no where to be found...." Usman da bai ma san abinda Maheer din ke cewa ba ya nufi parlon Ammi tun kan Maheer ya riskesa, yana bude kofar ya shiga yana kallon Ammi da ta daga kai tana kallonsa, yayi gathering courage yace "Su waye namu iyayen mu kuma?" Dai dai nan Maheer ya shigo parlon yayi gripping hand dinsa ya fitar da shi daga parlon, Ammi ta bi su da kallo as if trying to understand abinda Usman yace, can ta kalli Hajja da ita ma ta bi su da kallon mamaki, Mama ladi tace "Kamar yaya su waye nasu iyayen, ko dai wiwi suka bashi a kotun?" Ammi bata san sanda ta mike ta fice daga parlon da sauri ba, tsaye ta gansu corridor Usman ya hade kansa da bango Maheer was standing by his side looking confused as well, Ammi bata ce masu komai ba kamar yanda su ma basu ce mata komai ba, ta sauka downstairs Maheer ya bi ta da kallo, Aunty Mariya ta share hawayenta da sauri ganin yanda Ammi ta sauko downstairs tace "Ina kuma zaki Ammi?" Ammi bata ce mata komai ba ta fita, parlon da Abba ke zaune ta nufa, tana shiga ciki ta tsaya nan bakin kofa tana kallonsa tace "Boye min dalilin fasa auren Mayraah zaka yi?" Abba dake ta kallonta, ya ɗan sauke ajiyar zuciya, he knows she will definitely find out shi yasa ma da Aunty Mariya ta shigo tana ce masa kar a gaya ma Ammi yayi shiru don yasan wannan labarin kuma Allah kadai yasan iya inda ya tafi a yau din nan, gani yake har makota yanzu sun samu wannan labarin tunda ba a san ta inda ya billo ba, ya mike ya nufeta ya kama hannunta making her seat down kan kujera ganin she is palpitating, yayi kasa da murya yace "Ki kwantar da hankalinki Ammi, komai zai daidaita in sha Allah" Ammi na girgiza kai da kyar, hawaye na sauka idonta tace "Ka gaya min me ke faruwa, ina son ji daga bakin ka, menene yasa aka fasa auren Mayraah?" Abba ya dake yace "Allah ya ga zuciyar mu, bamu yi abinda muka yi don cutar da kowa ba, we did this out of our good heart, we only wanted the best for Mayraah, we didn't mean to be deceitful to anyone, Allah ya san intention dinmu...." Ya kasa ci gaba ya dinga kallon Ammi cike da tausayinta, he wish rana me kama ta yau bazai taɓa zuwa ba, the secret they kept for almost 23 years is now no longer a secret, ya dafa Ammi ganin she is more than shock, yace "Our main priority now is Mayraah, kada mu bari ta shiga damuwar da zai iya mata illa because it won't be easy mutanen da kake gani a matsayin iyayenka rana daya a tashi ace ba su ne iyayenka ba, she needs us the most in this trying time, and in sha Allah we will continue being the parent figure we are to her" mikewa Ammi tayi hawaye na sauka idonta a hankali tace "Zuwa yanzu duk an san ba mu muka haifi Mayraah ba kenan?" Bata jira cewar Abba ba ta juya zata fita daga parlon amma tun kan ta kai bakin kofar taga kofar da ma parlon na juya mata gaba daya, Abba ya nufeta da sauri... Mayraah ta dinga bin sa da kallo har ya kashe motar ya sauka, bata taɓa jin tsoro irin na wannan lokacin ba, ya zaga side din da take zaune ya bude motar, duk da yanda gabanta ke mugun faduwa ta marairaice cikin rawan murya tace "But i don't understand the meaning of this sir, ina ne nan ka kawo ni plss? This i almost 8pm, nasan ana ta nemana a gida" Tana kai wa nan ta fashe masa da kuka sosai, Musharraf dake ta kallonta yace "Kin zata son da nake maki iya baki kadai ya tsaya? An gaya maki na taɓa yi ma wata mace irin son da nake maki banda mahaifiyata? You think i have d strong heart to loose you just like that? You think bazan yi duk wani abu da zai sa in mallake ki ba?" The way he is talking kadai ya isa ya kara tsoratata, ita dai ta kasa cewa komai sai kallonsa take da manyan idanuwanta, kawai taga ya kamo hannunta ya sauko da ita daga cikin motar ya kulle, bugun zuciyarta ya tsananta she was so afraid of him a moment din nan, he doesn't look the gentle Dr Musharraf she knows, bin sa kawai take yana rike da hannunta, she don't think he is even okay, sai da ya fara kunna solar din gidan sannan suka iso entrance din parlon gidan, ta ga ya ciro makulli ya bude kofar, suna shiga ya sa ma kofar key ya zare, bata san sanda ta fashe masa da matsanancin kuka ba ta durkusa gabansa tana girgiza kai tace "Na shiga uku, sir don girman Allah tell me the meaning of this? Ina ce gobe ne fa daurin aurenmu, menene ya sa kuma zaka kawo ni wani waje da daddaren nan daga ni sai kai?" Musharraf ya girgiza mata kai yace "They are not prepared su daura mana auren gobe...." Yana fadin haka yayi hanyar dakunan dake parlon, Mayraah that was so confused ta bi sa da kallo zuciyarta na bugawa, gashi ya amshe mata waya ya kashe tun suna hanya, tayi zaman dirshan a wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka cikin tashin hankali, ko dai dama ba sonta Dr Musharraf yake ba kawai yaudaranta yayi, sai kusan karfe takwas da rabi ya fito daga dakin da ya shiga, yanzu kam wani mugun tsoronsa take ji har cikin ranta, yana kallonta yace "Tashi ki je kiyi sallah" Ta kasa kallonsa tsabar tsoro kuma bata motsa daga inda take ba, yace "Ba ki ji me nace bane" Mikewa tayi zuciyarta na bugawa, ya nuna mata daki da zata shiga, kamar munafuka ta shiga inda ya nuna mata tana waigensa. Har Mayraah ta idar da sallah hawayen dake sauka idonta bai tsaya ba, ta takure waje daya saman darduman da take zaune wasu sabbin hawayen na saukowa idonta, what will she tell her parent and her brothers, ina zata ce masu ta je tun wajen karfe biyar har gashi yanzu tara ake nema na dare, kafin su zo nan tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi a hanya, yanzu idan yace zai maidata gida ai sai wajen goma da rabi kilan za su isa ko sha daya, is he even ready to take her back home today? Tunanin hakan ya sa ta fashe da kuka sosai, bude kofar dakin aka yi, ta hadiye kukan da take ta koma baya a tsorace taki barin su hada ido da shi, ya shigo cikin dakin yana kallonta, ta sunkuyar da kanta hawaye wasu na bin wasu a cheek dinta ga wani faduwa da gabanta yake, ya duka dab da ita ya ajiye cup din fresh milk dake hannunsa a gefenta, he was just staring at her for almost a minute, cikin raunin murya yace "Saboda ina sonki yasa nayi haka Mayraah, wallahi i can't imagine me without you, ni kaina bansan irin son da nake maki ba Mayraah, plss kiyi min uzuri i only have this option...." Sai a sannan ta daga idanuwanta da suka yi ja tana kallonsa, kamo hannunta taga zai yi tayi saurin matsawa a tsorace without noticing d cup he kept by her side ta wuntsular da shi gaba daya milk din ya malale kasa, tun kan ya dagata har yayi soaking hijab din jikinta, yayi kasa da murya yace "I am sorry" Ta dake muryarta na rawa tace "Bana son kana taɓa ni don ni ba muharramarka bace" tana fadin haka ta juya masa baya duk da yanda gabanta ke faduwa, kallonta kawai yake, can ya juya ya fita daga dakin, Mayraah ta shiga bandaki da sauri ta cire hijab din jikinta, er doguwar riga ce a jikinta mara nauyi, ta wanke hijab din da detergent da ta gani a bandakin snn ta shanya inda taga towel a ajiye, har zata fito sai kuma ta koma ta dau towel din ta lullube jikinta da shi tana fitowa dakin ta gansa yana goge inda madaran ya zube, ta sunkuyar da kanta ta koma daya side din ta zauna kan carpet tana kallon agogon dakin, bayan ya gama goge wajen ya fita da mop din. Mayraah bata sake ganin Musharraf ba har kusan sha biyun dare, sau uku bacci barawo na sace ta tana farkawa a tsorace don babu kwanciyar hankalin yin bacci, ga duk tunaninta yana wajen Amminta, ko wani hali take ciki yanzu, daga karshe ganin karfe daya yayi ta mike a hankali ta nufi kofar dakin ta bude making sure bai yi ƙara ba, ta dinga bin corridor din dakunan da kallo, can tana tafiya a hankali ta shiga parlon gidan, a mugun tsorace da shock ta koma baya ganinsa kwance tsakiyar parlon idonsa a lumshe daga shi sai singlet with 3 quarter, ga empty kwalaben alcoholic wine guda uku a gefensa da roban fresh orange juice wanda shi kadae ne bai gama shanye wa ba, tsabar gigicewa bata san sanda ta karasa parlon ba don tabbatar da kwalban me take gani haka, ta durkusa ta dau kwalba giyan daya ta zaro ido tana karanta rubutun jiki, bata san sanda ta saki kwalban ba har sai da ya tarwatse tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" mikewa taga yayi zaune da sauri yana kallonta da jajayen idanuwansa, a guje ta tashi ta koma dakin da ta fito jikinta na rawa zata saka key amma taga babu key jikin kofar, ta durkushe kasa tana zaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" Bude kofar dakin taga yayi ta mike da gudu ta koma can karshen gado ta fashe da kuka don tsoro ta kasa cewa komai ta hade hannuwanta biyu tana kallonsa, kana ganin idanuwansa kasan he is drunk amma kuma he is calm at the same time duk da tafiyar ma da kyar yake yi amma he is not staggering, saboda gigicewa Mayraah bata san sanda ta shige bayan labule ba da taga ya nufota tana cewa "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri sir" Ya bude labulen ya janyota ta rirrike hannunsa cikin kuka tace "Nooo don Allah ka rufa min asiri sir, i am begging you pls..." Yayi hugging dinta cikin calm voice dinsa that is shaking yace "Kar ki bari a rabamu Mayraah, i don't know what will become of me, i...." Kasa ci gaba yayi, ita kuwa ko ina na jikinta rawa yake, ya jinginar da ita da bango underneath his breathe yace "Say something pls wife" Bakinta na rawa tace "Bazan bari a rabamu ba, i promise you, trust me" Yana kallonta da lumsassun idonsa yace "Can i kiss you pls?" Ta rike hannunsa ta wani zaro ido har sannan jikinta na rawa amma cike da karfin hali ta dake ta masa murmushi tace "Not now, u need to brush and freshen up first, i just caught u with bottles of wine isn't it...." Ya hade goshinsa da nata, da kyar yace "Orange juice was the last i drank..." Ai kam she could perceive the flavor of orange as he speaks, bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, she struggled to free her self amma ta kasa saboda irin rikon da yayi mata, hawaye ya dinga sauka idonta duk jikinta na rawa, bata kara gigicewa ba sai da taga ya fara canza salo, bata san sanda wani dakewa ya kuma zuwa mata ba tace "Ermm, i am very hungry pls sir, ina son in ci abinci kasan ban ci komai ba" Tana fadin haka kuwa ya saketa, she was still shaking don lokaci daya gaba daya yanayinsa ya canza, kamar me counting din words dinsa yace "Should... i.... get you some fresh.... Milk?" Ta gyada masa kai da sauri bakinta na rawa tace "Yes, yes yes plsss, i need it" Juyawa yayi ya nufi kofa, ta fara kalle kallen dakin, tana ganin ya fita ta nufi bandaki da gudu ta shiga taga babu key shi ma a ciki, sosai hankalinta ya tashi ta sake fitowa a gigice ta fita daga dakin, sauran dakuna uku dake corridor duk ta ji su a kulle an sa makulli, ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku, wayyo Ammi" Tana nan tsaye sai gashi ya taho rike da cup din fresh milk din, ta sauke hannunta ta hadiye kukanta da sauri trying her best to stay calm duk da yanda kirjinta ke heaving, ya nufota yana mika mata milk din, Mayraah ta amshi cup din tana kirkiran murmushi tace "Thank you so much, babu bread or chin chin?" Jingina yayi da bango alamar tsayuwar na neman gagararsa yace "Ba...bu" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Ohk, let me sip it little by little don yayi sustaining dina" Yana kallonta da idonsa da suka dawo so sexy murya can kasa yace "Ohk, ok..." Dukawa tayi nan kasa ta zauna tana satan kallonsa ta kai cup din baki tana kurban madaran da taji sa kamar magani a bakinta, da kyar ta hadiye banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, still bata fasa satan kallonsa ba taga shi ma ya zauna nan kasa yana facing dinta kamar zai hadiyeta saboda kallo, yau sai taji bata son kamshin turarensa dake kara mata sonsa a da, tunanin yanda zata janye hankalinsa daga abinda taga alamar yake son yi ta shiga yi don bata ga alamar kuka da pleading dinta zai canza masa wannan ra'ayin ba she just need to use her brain, shi ko bai fasa kallonta ba, Can dai dubara ya zo mata bayan ta kara kurban madaran a hankali tana kirkiran murmushi tace "But tell me sir, me yasa kake tunanin za a raba mu bayan kasan ina sonka sosai, kai ma kuma kana so na" Ya gyara zama kamar me rada yana maganar da daddaya da daddaya yace "Ba a son mu yi aure Mayraah, ance ba su Ammi da Abba bane suka haife ki, they said they are not ur Biological parent...." Mayraah ta sauke cup din bakinta tayi still tana kallonsa babu ko kiftawa jin abinda yake cewa, ya kalleta yace "Ko in kawo maki note din da aka dinga kawowa gidanmu akanki" Mayraah ta maida cup din milk gefenta tana gyada masa kai tace "Kawo min" Mikewa yayi taga ya shiga parlor this time around he is staggering alamar giyan ya fara hitting dinsa hard, ta bi sa da kallo babu ko kiftawa abinda ya fada na kai koma a kanta, bayan few minutes sai ga shi ya dawo ya zube mata Envelopes har hudu a gabanta ya zauna yana kallonta, Mayraah ta dauki daya ta bude da sauri ta fara karanta content din, ta fi minti daya tana sake nanata karatun kamar dai tana son fahimtar abinda ake nufi, can ta dau wani ta bude shi ma ta nanata yafi sau hudu, haka Mayraah ta dinga bi tana karanta duk takardun cikin envelope din, kana ganinta kasan she is confuse at this point, Musharraf ya kamo hannunta yana murzawa a hankali yace "Abbanki bai musa ba, yace haka ne, ba su ne suka haifeki ba, shine dangin babana suka ce bazan aureki ba don baki da asali, Mayraah even if u were born out of wedlock ni Musharraf bazan taɓa rabuwa da ke ba, ko ma wacece ke a haka nake son ki nothing can ever change that, Baby don Allah kar ki bari a raba mu, kawai mu yi rayuwanmu just i and you... we can go to Abuja a daura mana aure daga nan i will take you to Maldives mu yi rayuwarmu a can ki haifo min cuties kamar ki, i know my Mami won't be against that...." Mayraah ta zame hannunta a hankali daga nasa don duk abinda yake cewa bata ma san yana yi ba, kawai abun da ta gama karantawa ne ke ta mata yawo a kai tana sake nanatawa a zuciyarta, bata san sanda ta matsa daga kusa da shi ba tana girgiza kai tace "Noo, kawai dai ana son raba mu ne amma Abba da Ammi su ne suka haifeni they are my parent, it's all a lie" lokaci daya har hawaye ya cika idonta, Kawai gani tayi ya rungumeta a rikice yace "Yes love, karya suke yi, kawai suna son rabamu ne, plss don't let that, permit me to show u how much i love you today, tomorrow and forever..." Tashin hankalin Mayraah ya dawo sabo fil ganin ya dawo mata kamar wani zautattce, ganin abinda yake kokarin yi, ta dake tana gyada masa kai da sauri tace "Toh, to, to amma pls ka bari in yi wanka, kai ma kaje kayi wanka first...."
_Double update for june 10_🎊
0 Comments