Mayraah Page 17 Complete Novel By khaleesat Haiydar

Mayraah Page 17 Complete Novel By khaleesat Haiydar

 


Page 17


Badiyyah na shiga dakin da su Haseenah suke bakinta har kunne ta gaida Aunties din Haseenah sannan ta ɗare saman gado ta zauna kusa da Haseenah da Zaliha tana kyalkyala dariya ta ba ma Zaliha hannu suka cafke, sannan ta juya tana kallon Haseenah ta rike haɓa tace "Amarsu ta ango, kin ga yanda kika yi kyau kike wani glowing kuwa? anya Maheer zai gane ki idan ya ganki irin wannan canji haka? Ke wai me ya samu wayarki ne nake jin sa a kashe duk sanda zan kiraki" Haseenah da ta hade rai ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya yanda Aunties dinta baza su jiyo ta ba tace "Badiyya duk ke kika ja bikina ya dawo kamar na wata gantalalliya mara galihu, ban taɓa ganin warce aka ma irin wannan auren da aka min ba ko a kauye, kawaye na sai dariya suke min a bayana saboda cika bakin da na dinga yi akan bikin nan, daga karshe wae ace babu wani occasion da aka yi, a whole of my wedding? gown din dinner da na ci burin sa wa ya tashi a banza a hofi, banda Zaliha dake tare da ni da depression ya kama ni wllh" Tana kai wa nan ta fara matsar kwallan baƙin ciki, Badiyya ta ɗan kyabe baki tace "Ni duk ba wannan zancen ba, ban ga kin turo min kudin Stuff din nan ba har yanzu abu kusan kwana uku yau fa" Haseenah tayi mata wani shegen kallo a fusace tace "Ai kya bari a fitar da ni daga gidan nan tukunna dai ko? Wato ina gaya maki matsalata irin ke bai ma shafe ki din nan ba alhalin duk ke kika janyo wannan abun dake faruwa, tun fa jiya har yau ban sa Maheer a ido ba a matsayinsa na mijin da aka daura min aure, ko damuwa ya gan ni ma kamar baya yi" Zaliha ta sauke ajiyar zuciya tace "Kema Badiyya yanzu ba lokacin wani magana bane, kwantar mata da hankali za ki yi before anything" Badiyya ta taɓe baki tace "To ba dai tace ta ji ta gani ba, duk yanda na so ta hakura da Maheer din nan Allah ya bata wani Haseenah taki fahimtata, don daga karshe ma gaba ta dauka da ni, ɗan uwana ne fa, kuma baza ta ce min ta fi ni sanin mugayen halayyarsa ba, kawai mu dai fatan alkhairi za mu maki... Yanzu dai naji Hajja na gaya ma Uncles dina zuwa nan da sha daya za a tafi kai amarya gidanta...." Haseenah tayi tagumi murya can kasa tace "Badiyya duk ba wannan ba, wllh tun shekaranjiya hankalina ya kasa kwanciya, bazai kuma taɓa kwanciya ba in har da yarinyar nan Mayraah, na kasa samun sukuni idan na tuna matsayinta yanzu...." Badiyya ta rike haɓa tace "Yanzu nake samun labari ashe dai ta dawo daga guduwan da tayi, in dai kan wannan karamar alhakin ce ki kwantar da hankalinki da kafarta zata sake guduwa na har abada kuwa, wai baki yi trusting dina bane, tunda har na san yanda na bi aka fasa auren da Dr Musharraf kinsan ai babu abinda bazan aikata ba, haba ashe shi yasa kwata kwata na tsaneta tun tana karama, dama babu abinda muka hada da ita er tsintuwa ce kawai warce bata da asali, wa ma ya sani ko cikin shege uwarta tayi ta haifeta sannan ta jefar da ita ta gudu, da gani kasan ba er halaq bace yarinyar, shine saboda rashin tsoron Allah har ake fifitata a kai na a family, ai kam wannan duk ya kare yanzu tunda na gano wacece ita" Sauka Badiyya tayi daga kan gadon ganin flask ta bude tace "Ni fa ko karyawa ban yi ba muka taho...." Aunty Fauziyya tace "Ai ko duk an fita da sauran kayan kumallon sai dai kije kitchen" Badiyya tace "Bari in hado shayin" Badiyya na fitowa daga dakin Aunty Mariya kuma na kokarin shiga don sanar ma yan uwan Haseenah yanzu za a tafi kai ta gidanta su shirya, Badiyya taki barin ta hada ido da ita tayi saurin barin wajen ta sauka downstairs, Usman ta hango zaune kan dinning area, lkci daya ta juya ta koma sama ta fasa zuwa kitchen din..... Kaya kawai Badiyya ta canza ta fess uban turare ta yi daurin ture ka ga tsiya tana taunar cingam, hannunta rike da Mayafinta da handbag suka fito daga daki tare da yan uwan Haseenah da ita kanta Haseenar dake sanye da lapaya ta rufe rabin fuskarta, sai da aka fara kai ta tayi ma Ammi sallama sannan aka kai ta dakin Hajja, Badiyya ta zauna kusa da Hajja kamar zata shige jikinta, bayan Hajja ta kara yi ma Haseenah nasiha yan uwanta suka fita da ita daga dakin, Badiyya ta mike tana kallon Hajja tace "Kinga ki bani makulli kawai, don daga can gida zan tafi bazan dawo gidan nan ba gaskiya" Hajja tayi kasa da murya tace "Aa Badiyyah, ke dai ki dawo don sai gobe za mu tafi gida gaba daya har Ladi, so nake in kara ganin yanayin jikin Ammi yau" Badiyya ta wani murguda baki tace "To ina Mama Ladin?" Hajja tace "Kilan tana can gantali gidajen makota, daga zuwa unguwan mutane ta shiga gida yafi a kirga yanzu haka" Badiyya tace "Gaskiya ni dai gwara in koma Bichi in har da ita za mu tafi gida, wai ba an gama bikin ba me kuma take jira?" Hajja tayi kasa da murya tace "Banda abun ki ai jiya aka yi biki Badiyya, nasan nan da gobe zuwa jibi zata koma ita ma" Badiyya ta juya ta fice daga dakin tana murguda baki... Aunty Mariya na kallon Mayraah dake dakin Ammi tace "Ni ma kaina ai ba zama zan yi ba, ana kai ta zan juyo" Ammi dake zaune dakin tana jin su tace "Ki bar ta kawai Mariya tunda tace baza ta ba, kinga ita ma ba dadin take ji ba ai, daga baya idan Allah ya nufa sai taje ganin dakin amarya" Aunty Mariya tace "To shikenan sai na dawo" Dama tayi insisting ne Mayraah ta shirya su tafi don bata son tayi feeling neglected duk gidan an tafi kai amarya babu ita, don yanzu kamar taki sakin jiki a gidan, komanta sanyi sanyi take kuma a dar dar kamar dai bakuwa, tuni duk gidan aka watse kai Haseenah dakinta, Mayraah damuwar ta ya kasu kashi kashi yanzu amma babban abinda yafi tsaya mata a rai shine yanda bata samun Musharraf a waya, tun wayewar gari ta kirasa ya fi a kirga da wayar Ammi amma sai taji wayarsa a kashe, tana gama kiransa dama take clearing kiran a call log kar Ammi ta gani tunda tana da numbersa... saboda yanda ta sa abun a rai har ji tayi kirjinta ya fara mata ciwo, tana kwance bayan azahar idonta a lumshe duk da ba bacci take ba Ammi ta shigo dakin, Ammi ta zauna kusa da ita tana shafa kanta a hankali tace "Bacci kike daughter" Mayraah ta bude idonta sannan ta mike zaune tana girgiza mata kai, Ammi dai sai kallonta take, Abba ne ya karaso cikin dakin, lkci daya Mayraah taji zuciyarta ya karaya bayan sun hada ido, amma tayi kokarin ganin hawayen da ya makale idonta bai taho mata ba, Abba ya karaso har kusa da gadon he couldn't even look at her in the eyes again, bayan shirun few seconds yayi karfin halin cewa "How are you feeling daughter?" Ta kasa amsa masa sai gyada kai kawai tayi don tana buda baki tasan zata fashe da kuka, Ammi ta kalli Abba a hankali tace "Bacci take ne, anjima in ta tashi sai ku yi magana..." Abba dai bai ce komai ba, bayan few seconds ya juya ya fita daga dakin, Ammi ta mayar da ita ta kwantar tace "Or you need anything?" Mayraah ta girgiza mata kai hawaye na gangaro mata, Ita ma Ammi tuni hawayen ya kawo idonta, Mayraah ta riko hannunta tace "Ammi kin sha maganin?" Ammi ta gyada mata kai sannan ta mike ta fita daga dakin tana goge hawayen dake zuba idonta. Bayan Magrib Mayraah na zaune dakin Ammi ta idar da sallah, zuwa sannan babu kowa gidan duk yan biki sun watse, Ammi na parlonta ita ma ta idar da sallan tana zaune kan darduma, Mayraah taji Ammi na cewa "Baka tafi gidan ba bawan Allah?" Muryar Maheer taji yace "Zan duba jikin Mimi ne" a hankali Ammi tace "Naga ma bata cin abinci yanzu, ko maganin cin abinci za a bata?" Maheer yace "Bari in tambayeta ko da abinda take so ne" Ammi bata ce masa komai ba ya karasa cikin dakin, tun da ya shigo Mayraah bata bari sun hada ido ba, ya zauna gefen gado yana kallonta don tunaninsa addu'a take saman darduman, jin bai ce komai ba ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta sauke idonta tace "Ina yini" Yace "Kin gama?" Ta gyada masa kai, yace "To tashi mu je ki fadi abinda kike so a siya maki" Ta ɗan kallesa tace "Ai na ci abinci" Shiru yayi yana kallonta, don komin abincin da ta ci bata taɓa ƙin bin sa ya siya mata ko ice-cream or shawarma in zai fita siya ma Ammi fruits da daddare, jin yayi shiru ita dai taki dago kanta tana ta wasa da fingers dinta, she was soo uncomfortable, a hankali taji yace "You are now trying to tell the world i am no longer ur brother Mimi, and u forgot i have been ur brother for good 22 years, me yasa kike son canza hakan yanzu?" Hawaye ya kawo idonta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya dago ta, ta kwace hannunta tana hawaye, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, cikin rawan murya tace "Kayi hakuri" Ya ma rasa abinda zai ce mata, bayan few seconds a hankali yace "Mu je" Bata bari sun hada ido ba tana goge hawayen dake sauka idonta ta nufi kofa ya bi bayanta, suna fitowa parlor Ammi ta dinga kallonsu, yace "Ammi i want to get her something sai in dawo da ita yanzu" a hankali Ammi tace "Ka bar er mutane fa a gida Maheer..." Yace "Ai kawayenta suna nan, kuma sai naje ma zan maida su various houses dinsu" Ammi ta kalli Mayraah tace "To sai kun dawo Mimi" yana gaba ta bi bayansa suka fita daga parlon, mamaki bai cika Maheer ba sai da yaga all through the ride ko tari bata yi ba, Mayraah da har sai ya gaji da labarinta idan suna mota tare, sosai ya ji abun ya damesa yanzu, yayi parking dai dai wani eatry yana kallonta a hankali yace "Shawarma da me zan siya maki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Anything" Bayan few seconds ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido, yana dawowa motar ya ajiye mata abinda ya siyo mata sannan suka bar wajen, duk da hanyar da ta ga ya nufa da ita bata ce komai ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin yayi parking dai dai gate din gidansa, wayarsa ya dauka yayi dialing number Haseenah tana dagawa yace "Tell ur frnds ina jiransu zan ajiye su gida yanzu" Da mamaki Haseenah tace "Ban gane ba, ina abokan naka? Kana nufin yanzun ma baza a siyi baki ba da sauransu?" Maheer yayi shiru kafin yace "Bakin wa za a siya?" A fusace Haseenah tace "Ni wallahi na gaji da walakancin da kake min Maheer dama ba sona kake ba ka aureni?" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, yace "No.... it's not like that Haseenah, kinga frnds dina yawanci a Abuja suke so duk sun koma saboda aiki, kiyi hakuri kawayen naki su fito in maida su gida, sannan su fadi nawa za a basu sai su turo account number" Cike da shagwaba Haseenah tace "Za ku yi magana da Zaliha idan sun fito" Yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, juyawa yayi ya kalli Mayraah, if it was before yanda tayi shiru haka da ya ja hancinta amma yanzu kam bai yi hakan ba, yayi kasa da murya yace "Tunanin me kike?" A hankali tace "Bacci nake ji" Yace "Ohk, yanzu zan maida ki gida ki kwanta, hope kina shan magungunan da na siyo maki tunda baki son alluran?" Ta gyada kai tace "Ina sha" Yace "Ohk" kawayen Haseenah hudu suka fito daga gidan har da Badiyyah, Maheer ya hade rai ganinta, Zaliha ta bude front seat tana washe baki tace "Ango ka sha kamshi" Gaba dayansu suka yi turus ganin Mayraah gaban motar, barin Badiyyah da ta bude baki da mugun mamaki, Maheer yace "Ku shiga in ajiye ku gida, it's getting late" Zaliha ta kirkiri murmushi ta koma back seat tare da sauran frnds din nasu, Badiyyah ta zaro ido tace "Aneesah na baki wayata kuwa?" Aneesah tace "Aa" Da sauri ta juya ta nufi cikin gidan tana cewa "Lahhh ban ciro sa a caji ba kenan" Badiyya na tuntube ta koma dakin Haseenah, tsaye ta ganta gaban madubi tana gwada kayan baccin da zata sa tana murmushi, Badiyyah tace "Ke kinsan da wa Maheer yake a cikin mota kuwa?" Haseenah ta juya da sauri tace "Aa" Badiyyah tace "Wllh er tsintuwar nan muka gani zaune gaban motarsa, wato duk maganganun da muka maki kan cewar ki ja masa aji yau akan abubuwan da ya dinga maki a biki har kin watsar kin wani kwaso kayan bacci kin zube kina zaba ko? To ai shikenan" Sosai gaban Haseenah ya fadi jin warce Badiyya tace mata sun gani a motar Maheer, ta dinga kallon Badiyyah ko kiftawa babu, tuni Badiyyah ta juya ta fice daga dakin ta koma compound tana ma mai gadi sallama sannan ta fita kofar gida, still tayi bakin gate ganin babu motar Maheer alamar ya tafi ya bar ta. 

Wajen karfe tara da rabi Mayraah na tsaye a kitchen kusa da gas tana dafa ma Ammi shayin da ta saba yi mata, dafa shayin take amma gaba daya hankalinta baya jikinta, rashin samun wayar Musharraf ya dameta sosai don har wani zazzabi take ji yanzu, to ko dai he doesn't need her anymore because of who she is, tunanin hakan yasa taji hawaye ya kawo idonta, sai yanzu ta sake tabbatar da son da take ma Musharraf na gaske ne, tana kokarin zuba shayin a cup bayan ta gama taji an bude kofar kitchen din ta juya, sosai gabanta ya fadi ganin Badiyya ce ta shigo, Mayraah tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take tana goge idonta zuciyarta na bugawa, dawowar Badiyya kenan gidan tun bayan da Maheer ya tafi ya bar ta, Badiyyah tayi wani dariya tana kallonta tana tafe hannu, can ta rike haɓa tace "Ohh wai Shege ya fi ɗan masu gida, to in ji dai yanzu kin gane cewar matsayina da naki ba daya bane a family dinmu, don ke ba kowa bace facce tsintattciya walakantacciya warce karuwar uwarta ta wuragar da ita a gefen masallaci! Banda ma rashin sanin wacece ke ai da baza ki fara soyayya da Musharraf ba don yafi karfinki nesa ba kusa ba, shima kuma ko a mafarki bazai so ya kula irin ki ba mara asali, dama ance rashin sani yafi dare duhu, ai irin su Dr Musharraf sai mu masu asali gaba da baya yan dangi yan gata ba wa enda aka jefar tun suna tsummam haihuwa ba...." Mayraah kasa juyowa tayi sai hawaye kamar an bude famfo, ihun da taji Badiyya ta kwala ne yasa ta juyawa da sauri, da kafa ya sa ya kwasheta sai ga ta rigijib a kasa sannan ya kulle kofar kitchen din, Mayraah ta tsorata sosai ga koma gefe tana kallonsa, tuni ya zare belt dinsa ya fara lafta ma Badiyya ta wajen kan belt din kamar an aikosa, Ihu Badiyya take iya karfinta tana kokarin tashi amma ta kasa tsabar yanda belt din ke shigarta ta dinga birgima kamar macijiya tana cewa "Na shiga uku na lalace, Hajjaaaa" Mayraah da duk ta gigice ta tafi kofar kitchen da zai yi leading dinka zuwa backyard din gidan zata bude ya daka mata tsawa yace "Kina budewa zan hada da ke" Makalewa tayi jikin kofar zuciyarta na bugawa tana kallon yanda yake dukan Badiyya ba kakkautawa, bude kofar kitchen din Aunty Mariya tayi a gigice don tana saukowa parlor ta fara jiyo ihu kamar daga kitchen, a sama kuma ba a jin komai, Badiyya na ganin Aunty Mariya cikin gigicewa ta dinga cewa "Wayyo Aunty ki shigo ki taimakeni zai kasheni, wallahi kasheni zai yi ki kira har da su Hajja da Ammi" Aunty Mariya na ganin abinda ke faruwa ta kullo kofar kitchen din tana murmushi ta koma parlor ta zauna, Sai da yayi mata lilis ya farfasa mata duk jikinta da belt har bata iya motsin kirki tsabar dakuwa sannan ya duka yana kallonta cikin husky voice da idanuwansa da suka canza launi yace "Ko kallon banza ki sake yi mata a gidan nan ki ga" Daga haka ya tsallaketa ya nufi kofar kitchen da Mayraah ke kokarin budewa ya hanata, da sauri ta koma gefe ta basa waje gabanta na faduwa, ya bude kofar ya nuna mata waje yace "Fita mu je" Ba musu ta fita da sauri, shi ma ya fita ya kullo kofar.....




MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Mayraah Page 18 By Khalesat Haiydar


Post a Comment

0 Comments

Ads


Click Here To Download This Book