Mayraah Page 3 Complete Novel By Khalesat Haiydar

Mayraah Page 3 Complete Novel By Khalesat Haiydar

 💖💖 *MAYRAAH*💖💖



By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻


3....



Musharraf ya ajiye glass din parfait din hannunsa yana kallon dattijuwar matar dake zaune opposite dinsa a parlon yace "But Mami is that really necessary? Ni kin san i know nothing about kayan amfanin mace" Mami dake danna wayarta tace "Ai kai da ita za ku tafi, ta fi kowa sanin abinda zata fi bukata, kaga kuwa it's necessary..." Musharraf yace "For how many days kenan za ayi siyayyan, naga ba abu kadan ake siya ba, gaskiya Mami ni kin san fa...." Sai kuma yayi shiru ya jinginar da kansa da kujera yana kallon mahaifiyar tasa ganin kamar she isn't even listening to him, Mami ta daga kai ta kallesa ta cikin glasses din idonta tace "Na san me?" Yace "Mami why not taje da driver din gidan nan su yi siyayyar sai ta sa Nikab" Mami tace "Saboda a garin gaɓa gaɓa ake ai da iyayenta za su bari ta bi driver siyayyan lefe" Ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Mami kinsan every nook and cranny din kano akwai frnds dina bana son a gane min mata tun before marriage" Mami ta masa wani kallo tace "To sannu me mata, shopping din da a kwana daya duk za a yi a gama shine za ka hadu da each and every frnd dinka na cikin kano?" Yayi kasa da murya yace "Mami amma me yasa su Aunty Ruma'isa baza su hada kayan akwatin ba? Naga ai duty dinsu ne yin hakan" Mami tace "A yanda ka ki zabinsu shine za su hada maka lefe? Or are you dreaming? Yaushe rabon da ka ga Ruma'isa ko Sajida a gidan nan? Hatta Aunty Halima ta dauke kafa a gidan nan ai for long" Musharraf dake ta kallonta da mamaki yace "Oh really?" Mami tace "Don haka ka sanar ma yarinyar ranan asabar sai ku je ku siya abinda duk take so na kayan akwatin ta, dama da Baby ko Fatima suna nan su za su yi, ni kuma bana son stressing any of my frnds in daura masu wahala" Musharraf yayi shiru, can ya ɗan kalli Mami da har ta maida hankalinta kan abinda take a wayarta yace "Mami or should i send her the money su hada lefen a can gidansu?" Mami ta mike tace "Do what suit you sweetheart" Daga haka ta bar parlon, ya bi ta da kallo.... 

Mayraah ta ajiye wayar hannunta a gefen gado, lokaci daya duk mood dinta ya canza, bayan kusan minti biyu ta kalli Maheer dake kallo cikin system din sa, kamar zata yi kuka tace "Yaya" Ya daga kai ya kalleta yace "Oh har kin gama wayan" Tace "Wai kasan me yake ce min?" Maheer yayi pausing kallon da yake paying attention to her yace "No" tace "Wai za mu je siyayyan lefe tare, is it done that way plss?" Maheer ya buda ido yace "Of course, ko Haseenah tare muke zuwa siyayyan lefe ai...." Mayraah ta kara hade rai ta jingina da gadon ta rungume hannunta tace "Ni dai bazan iya bin sa ba" Maheer yace "Why?" Tace "kunya nake ji" Maheer ya buda baki, sai kuma yace "Ke fa bush gal ce Mimi, ai yanzu haka ake yi, kinga u will be privileged to chose whatever u want, komai na box din choice dinki zai zama ne" Ta marairaice tace "Yaya baza ka gane ba wllh kunya nake ji" Yace "To ki tafi tare da wata kawarki mana idan har ya amince" A hankali Mayraah tace "Hamidah?" yace "Good, ku je tare da ita" Tayi shiru, can kuma tace "Ohk i will tell him, sannan kuma wai zai kai ni in gaida Maminsa next week, is it done that way?" Maheer yayi dariya yace "Ni ba ranan friday din nan zan kawo Haseenah ta gaida Ammi ba" Mayraah tace "Yaya wllh ni dai kunya nake ji, i can't face his mum" Maheer yace "You have to my dear, it's good ya kai ki ki gaisheta, ta san surkarta tun ma kan ayi biki" Mayraah tace "Amma fa ina ga Ammi bazata bari inje siyayyan lefe da shi ba" Maheer yace "Haba zata bari mana, ai ana yin haka yanxu" Wayarsa ce ta fara ring ya dauka yana kallon me kiransa don rabonsa da ita tun da ya baro gidansu tare da Mayraah shekaranjiya, Mayraah da duk abun duniya ya dameta ta mike ta dau wayarta tace "Sai da safe yaya" Daga haka ta fita daga dakinsa ta koma nata... Bayan ta gama shirin kwanciya tayi dialing number Musharraf, katsewa yayi ya kirata, a hankali tace "Sir i have come up with an idea" yace "Ohk, i am all ears..." Tace "Pls za mu iya zuwa siyayyan kayan da Hamidah?" A takaice yace "No" zaro ido tayi tace "But why? She is my close frnd" Yace "I said No" ta wani turo baki tace "sai da safe" Yace "Sleep tight" Ko amsa masa bata yi ba ta katse wayar ta shige cikin duvet dinta. Washegari da safe har Mayraah ta tafi makaranta bata da walwala, kawai zulumin yanda za ta fita ita da Musharraf zuwa shopping din lefe ne ya cika zuciyarta, ko baccin kirki bata yi da daddare ba don abu kadan take sa wa a rai ya dameta, bayan sun fito daga second lectures dinsu na ranan wajen karfe daya da rabi Hamidah na kallonta da damuwa tace "Lafiyarki kuwa Mayraah, naganki duk wani iri yau" Mayraah ta kalleta ta ɗan yi murmushi tace "Kaina ke ciwo, yanzu ma gida zan tafi bazan iya jiran lectures din karfe 4 ba" Hamidah tace "Subhanallahi, Allah ya sauwake, mu je in raka ki, Allah sa mu samu Napep nan kusa, the sun is scorching" A haka suka fita daga department din, wani Coursemate dinsu ne ya nufo su yana kallon Mayraah yace "Dr Musharraf yace ki samesa a karkashin wancan bishiyar" Sosai gaban Mayraah ya fadi ta kalli direction din da Coursemate din ke nuna mata, da ɗan tafiya daga department dinsu amma ba sosai ba, Hamidah tace "To Alhamdulillah kin ga babu rabon mu yi dogon trekking zuwa gate, shikenan ki gaida su Ammi Allah ya sauwake" Mayraah ta kalleta tace "Ameen nagode Hamidah" daga haka Hamidah ta koma cikin department Mayraah kuma ta nufi inda ta hango motar Musharraf tana tafiya a hankali, tasan ya kikkira wayarta ita kuma a gida ta bar wayar.... Tana isowa gun motar ta bude front seat ta shiga ta kulle motar, kallo daya tayi masa ganin yanda yake kallonta ta dauke kai tace "Ina yini" yace "Why are ain't you picking ur calls?" Tana wasa da zoben hannunta tace "A gida na bar wayan" yace "Saboda me?" Tace "Manta sa nayi" ganin yana reverse tace "I am not done with today's lectures" Yace "Ko ba Dr Nura ba?" Ta ɗan kallesa bata ce komai ba, yace "To baza kiyi attending ba" Har suka fita daga school din bata ce komai ba, yana driving calmly yace "Saboda baki son mu fita mu biyu kadai shine kika yi introducing frnd dinki a fitan namu?" Ta ɗan daure fuska tace "Fitan mu? To ai ban gaya ma Ammi ba har yanzu, kuma idan tace bazan bi ka ba ai bazan bi ka ba no matter what, so i only suggested ko za mu je da kawata ba tare da nayi shawara da Ammina ba, in kuma Ammi ta hanani ai kaga babu inda zan je" Lokaci lokaci yake kallonta har ta kai aya tayi shiru, ya gyada kai yace "Ashe bayan shiru shiru har da rashin kunya kika iya ban sani ba" Ita dai bata sake cewa komai ba kuma bata kallesa ba, sai da suka kusa gida yace "Me za ki ci?" Ta juya suka hada ido sai kuma ta sauke idonta kasa tace "Nothing, thank you" Fruits ya tsaya ya siya a wani wajen masu fruit, suna isa kofar gidansu yayi parking yana kallonta ta dau jakarta tace "Kayi hakuri idan abinda na fada ya bata maka rai..." jin bai ce komai ba ta ɗan kallesa, murmushi yayi yana shafa beard dinsa a hankali yace "Ki shiga ki sanar ma Ammi zan shiga in gaisheta da jiki" Da sauri tace "Ai ta samu sauki" Yace "I know, shi yasa ma nake son shiga in gaisheta" Ta kasa ce masa komai, sai kuma tace "But..." Yayi kasa da murya yace "Do as i say Mayraah" Ta kauda kanta, bayan few seconds ta bude motar ta sauka ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gida. Bayan kusan minti biyar ta dawo tana kallonsa tace "Ka shigo" Kashe motar yayi ya sauka yana rike da ledan fruits din ya bi bayanta zuwa cikin gidan, a main parlor din gidan ya zauna, Mayraah ta tafi kitchen tana kallon Sabeera tace "Aunty Sabeera ki kai masa ruwa da lemo don Allah" Sabeera tace "To Hajiya" juyawa tayi ta fito daga kitchen din ta wuce sama ya bi ya da ido, ba a dau lokaci ba Ammi ta shigo parlon bayan sun gaisa da fara'a take tambayarsa mutanen gida, yace "Suna lafiya Ammi, ya jiki?" Ammi tace "Ai naji sauki Alhamdulillah" Yace "To Allah ya kara lafiya" Ammi tace "Ameen" yace "To zan koma, dama zuwa nayi in gaisheki" Ammi tace "To ko ruwan ma baka sha ba ai" Yace "Aa nagode Ammi, ana jirana ne" Ammi ta mike tace "Bari in mata magana, don Allah ka gaida umman ka, ina gaisheta sosai" Yace "In sha Allah" Ammi tayi masa godiya sannan ta wuce sama, fita yayi daga parlon, ko da Mayraah ta fita kofar gida bayan Ammi ta sanar mata zai wuce bata ga motarsa ba don har yayi wucewarsa, ta juya ta koma cikin gida.


Ammi ta bude kofar dakin Maheer ta shiga da sallama, ya amsa yace "Baki kwanta ba Ammi?" Ammi tace "Ban kwanta ba" Karasowa tayi ta zauna kan kujera dake dakin tana kallonsa tace "Ka sake komawa gidan Hajja kuwa? Ina son sanin yanda ake ciki ne" Yace "Ko dazu naje har yanzu dai bata dawo daga Bichi da ta tafi ba" Ammi tayi shiru, can tace "Ya kake ganin za a bullo ma lamarin nan Maheer, ni duk kaina ya daure wllh" Da mamaki Maheer ya kalleta yace "Kamar ya kenan Ammi? Wai me yasa ake biye Badiyya ne..." Ammi ta katse sa tace "Marainiya ce Maheer, er kanwata ce duk yanda ku ke tunanin zan maku ita ma haka zan mata, wallahi abun ya tsaya min a rai, sannan bazan fifita Mayraah a kanta ba" Maheer yace "Don Allah Ammi ki bar wannan zancen, it's not even making sense sai kace wani wasan kwaikwayo, this is reality, abinda zai yiwu shi ake yi, ba ita wannan mutumin yace yana so ba, to don me za mu mayar da kanmu kananun mutane, don Allah ki bar issue din nan yayi sliding haka, ni wllh idan ta kuskura mu ka yi ido hudu da ita Allah sai na mata dukan tsiya tunda bata da kai" Ammi tace "Aa kar ka taɓa ta, tunda ku baku san meye maraici ba...." Maheer yayi saurin kauda zancen don ɓata masa rai ma yake, yace "Ammi gobe Haseenah zata zo gaisheki in sha Allah" Ammi tace "Toh, Allah ya kai mu lafiya" Yace "Ameen, and Mayraah ta sameni jiya da wata magana wai ita bazata iya gaya maki ba" Ammi ta maida attention dinta gaba daya kansa tace "Wace magana kenan?" Maheer yace "Gobe Saturday za su fita siyayyan lefe shine bazata iya gaya maki ba" Ammi tayi shiru tana kallon Maheer, bai bata daman cewa komai ba ya ci gaba "Kinsan ai yanzu haka ake yi, nima ba gashi tare mu ke hada kayan da Haseenah ba, so ba wani abu bane wannan" a hankali Ammi tace "To ai ban san ko Abbanku zai yarda ba" Maheer yace "Ni zan gaya masa da kaina, yanzu modern era mu ke, komai kuma tafiya yake da zamani" Ammi dai sai kallonsa take, yace "Kuma bikin na gabatowa zai kai ta ta gaida mahaifiyarsa, ni ba gashi zan kawo Haseenah gobe ta gaisheki ba" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "To dai duk ku gaya ma Abbanku ni ba ruwana" Murmushi yayi yace "Zan kirasa gobe da safe in sha Allah, naji yace next week zai dawo ko" Ammi tace "Haka yace" Mikewa tayi tace "Zan je in kwanta" Maheer yace "Allah ya tashe mu lafiya Ammi" Ta juya ta fita daga dakin ta kulle masa kofa. Washegari da ya kasance friday Mayraah bata je makaranta ba duk don tayi assisting Sabeera su yi girke girken da za a tarbi Haseenah, Fried rice ta yi da pepper chicken sai zobo drink da small chops, ganin da sauran time tayi cupcakes, babu abinda ke kara sa yayyinta maza ji da ita sai saboda iya girkinta, Mayraah is so perfect in making any sort of food, iya girki na daya daga cikin baiwarta, banda yanzu da ta shiga final year bata da time din kanta da kusan kullum ita ke ma Maheer girki, haka ma Umar dake bribing dinta tayi masa in dai yana gari, Usman ne kadai ko a jikinsa in an basa ya ci idan ba a basa ba ko kallo abincin bai ishesa ba, dama kuma ba wai suna wani shiri bane can da shi, Maheer ne favourite dinta sae Umar idan ya dawo, Wajen karfe sha biyu Ammi ta shigo kitchen din tace "Su Mayraah abun nema ya samu, wannan duk na Antyn taki ce haka" Mayraah tayi dariya tace "Abinci kala daya fa kawai muka yi Ammi" Ammi tace "To sannunku da aiki" Daga haka ta bar kitchen din. Bayan sallan juma'a Maheer ya iso gidan tare da Haseenah, tun suna hanya yayi ma Mayraah text yace sun taho, tana jin shigowar motarsa compound ta dau gyalenta ta fito ta tsaya balcony, shi ya fara sauka a motar sannan Haseenah ta sauko, sanye take da tsadadden atamfa an mata riga da skirt, sai mayafi medium size da ta yafa hannunta rike da jakarta, tayi ma fuskarta very light make up, tun daga nisa Mayraah ke hango gold din fingers dinta wa enda ke ta daukan ido, tayi kyau sosai ba karya, Mayraah ta sauka balcony din ta karasa har gun motar da fara'a tace "Sannu da zuwa Aunty" Maheer dai yayi gaba zuwa cikin gidan, ba tare da Haseenah ta kalleta ba tana taunar gum tace "Yauwa" Daga haka ta bar ta wajen tsaye ta bi bayan Maheer, Mayraah ta bi ta da kallo irin na mamaki, can dai ta bi bayanta tana tafiya a hankali, Mayraah na shiga parlor ta tarar har Haseenah ta zauna shi kuma Maheer ya haura sama, hada ido suka yi Mayraah ta dauke kai ta wuce sama ta tafi dakinta tayi kwanciyarta, bayan kusan minti ashirin aka bude kofar dakinta, ta yi saurin kulle ido don har taji kamshin turarensa, ya kulle kofar yana kallonta yace "Mimi" Ta bude ido da kyar kamar irin baccin nan take, yace "Why did u come upstairs?" Ta mike zaune tana murza ido cike da shagwaba tace "Yaya kaina ciwo yake tun safe kasan nake ta aiki fa, kuma da na shigo ban san sanda ma bacci ya daukeni ba" Yace "Ohk ki fito ku yi sallama i am taking her back home now" Mayraah ta marairaice tace "Yaya my head is so heavy, i am not feeling fine" Shiru yayi bai ce komai ba, can ya juya ya fita, komawa tayi ta kwanta, ba a dau lokaci ba ta sake jin an bude kofa ta juya, ya shigo cikin dakin ya ajiye mata paracetamol a bedside drawer da bottle water yace "Ki tashi ki sha, sai na dawo" Daga haka ya fita daga dakin. Maheer na ajiye Haseenah a gidansu tana shiga compound tayi dialing number Badiyya, Badiyya na dagawa Haseenah na buga kirji tace "Badiyya, ni wannan cousin din taki zata walakanta yau?? Ni zata ma kallon banza tayi wucewarta kamar ta ga kashi saboda naje gidansu?" Badiyya tace "Oh kin je gidan kenan yau?" Rai bace Haseenah tace "Wallahi wallahi da nasan abinda Maheer zai kai ni gidansu kanwarsa ta min kenan da ban je ba, babu abinda zai fara kai ni gidan komin tashin hankalin da za mu yi da shi, ita kanta uwar tasa kamar bata yi wani farin ciki da zuwana ba don ko minti biyar bata yi ba a parlon bayan mun gaisa tayi wucewarta sama aka bar ni daga ni sai TV da abinci a gabana kamar abinda ya kawo ni kenan" Badiyya tace "Atoh, shi yasa nace kice masa ba yanzu za ki je ba, kyau ace ina gidan kika zo" A fusace Haseenah tace "I feel so humiliated Badiyya, yarinyar da a haihuwan kaji na haifeta zata min wannan walakancin? Me aka yi aka yi ta?" Badiyya tace "Yanzu dai ki bari za mu yi waya jirana ake, nima ai yau zan koma gidan Hajja, Mayraah kuwa ko da ni Badiyyah ban auri Dr Musharraf ba ba fata nake ma kaina ba, to wllh sai dai taga wata can daban ta auresa amma ba ita ba, balle in sha Allahu ni ce matarsa, in Allah ya yarda.. " Haseenah tace "Ai wllh in har kika bari ta auri lecturer din nan ni na ma raina ajinki da capacity dinki, baki cika Badiyyan da duk muka sani ba in har hakan ta faru" Badiyya tayi murmushi tace "Ke dai za mu yi waya" Daga haka ta katse wayar.

 Ranan asabar kamar yanda Mayraah tayi ma Hajja alkawari karfe goma ta gama shirinta ta sauko downstairs don Ammi na parlor tare da Usman, Mayraah ta rakube jikin kujera tana kallon Ammi tace "Ammi na shirya" duk tunanin Ammi siyayyan za su je yi, ta kalli agogo tace "Ya zo ne?" Mayraah tayi jim tana tunanin yaushe tace ma Ammi Musharraf zai zo, can tace "Ammi ni fa gidan Hajja zan je" shiru Ammi tayi tana kallonta kafin tace "Ba naji ance za ku je siyayya ba, kuma me za ki je yi gidan Hajja" Mayraah ta ɗan ɓata rai kamar zata yi kuka tace "Ammi na mata alkawari zan je yau fa, kuma ma ai ba yanzu za mu yi siyayyan ba sai da yamma" Ammi tace "Aa ki hakura da zuwa gidan Hajja, ki bari ranan da baki da lectures sai mu je tare" Usman dake kallon Tv ya kalli Ammi yace "Saboda me?" Ammi tace "In zan je sai mu je tare kawai" Mayraah ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba amma abinda Ammi tace bai mata dadi ba, Usman yace "Ni ma ai can zan je yanzu, ki bari in ajiyeta sai mu dawo tare idan zan dawo tunda ni ba dadewa zan yi ba, i will be going to Zaria later"

Ammi ta kalli Mayraah don har cikin ranta taji wani iri ɓata ran da tayi, Ammi tayi kasa da murya tace "To ku je tare, amma ki tabbatar kin biyosa idan zai dawo" a hankali Mayraah tace "To Ammi, Nagode" Kallon Usman Mayraah tayi tace "Yaya yanzu zaka tafi?" Usman ya kalleta yace "What is ur business?" Nan da nan Ammi ta hade rai tana kallonsa tace "Kai komai masifa bawan Allah" Mikewa Mayraah tayi ta tafi kan kujera ta zauna bata sake cewa komai ba, Ammi tace "To meye laifi ma don ta tambayeka banda fitinarka tayi yawa" Ya mike yace "To idan bata da lectures din sai ku je tare, sai na dawo" Mayraah ta zaro ido da sauri ta mike tace "Yaya don Allah kayi hakuri" tuni ya fice daga parlon, Ammi ta tabe baki tace "Bi sa ku tafi" Mayraah ta bi bayansa da sauri.... Tafiyar minti talatin suka yi suka iso gidan Hajja, tsabar ba dadewa zai yi ba a waje yayi parking motarsa suka gaisa da mai gadin gidan ya shiga ciki Mayraah na biye da shi, parlon Hajja cike yake da yaran makota sun shigo kallon cartoon, Hajja na ganin Usman tace "To duk ku tashi ku tafi jikana ya zo, maza ku tafi" Babu wanda ya motsa cikinsu kamar basu ji ta ba, Usman yace "Kai ba magana ake maku ba" lokaci daya duk suka mike suka fita, Hajja ta marairaice tace "Ni na gaji da wahala gaskiya, kaga da baka sa baki ba wllh baza su tashi ba, ko na koresu basa tafiya sun maida ni wata mara makabuli, kakanninsu na can suna hutawa ni kuma sai a zo nan a dameni a cika min parlor har da almajirai, tunda suka kyallara ido suka ga Badiyya ta fita duk suka shigo" Hajja ta zaro ido ganin Mayraah tace "Dama tare ku ke, sannunku da zuwa, ai ko kin cika alkawari" Mayraah na murmushi ta karasa ta zauna kusa da Hajja ta gaidata, Hajja ta amsa da fara'a tace "Ina Ammin taki" Mayraah tace "Tana gaisheki" Usman ya zauna yace "Ina kwana Hajja" Hajja tace "Lafiya lau ya aiki" Yace "Alhamdulillah" Bude kofar parlon aka yi sai ga Badiyya ta shigo, Usman ya bi ta da ido kamar zata wuce sai kuma tace "Ina kwana yaya Usman" Yace "Lafiya lau" Mayraah na kallonta tace "Ina kwana Aunty Badiyya" Tuni Badiyya har ta shige daki, Hajja ta girgiza kai murya can kasa tace "Na gaji da yarinyar nan, ko sallama fa bata min ba ta fita, yau da asuban fari naga tana ta hada akwatunanta na kasa hakuri na leka daki nace ina kuma zata, wai zata koma gidanku..." Sosai gaban Mayraah ya fadi tana kallon Hajja, Usman yace "Zata koma gidanmu tayi me?" Hajja ta rufe baki da sauri tace "Kul kar ka sake cewa haka, ba fa bare bace, yar uwarka ce ta jini, don tace zata koma gidanku ai ba wani abu bane, nasan babu abinda Mamuda zai ce kuma bazai hana ta zauna masa a gida ba, tun yaushe ake son ta koma can din don ku sa mata ido ta rage abubuwan da take amma fir taki, tunda yanzu Allah ya so mu don kanta ta dawo tace zata sai a bar ta ta tafi kawai, dama anjima nake son kiran Ammi" Usman yace "Karya take yi, akwai wani munafurcin da take kullawa, banda haka bazata ce zata dawo gidanmu ba" a fusace Hajja tace "O'o Allah mu yi mata kyakkyawan zato mana Usman" Usman yace "Allah ya kawo ta lafiya, dama zuwa nayi in gaisheki na kwana biyu ban zo ba, yanzu sauri nake zan tafi Zaria" Hajja tace "Ai ko nagode Allah maka albarka" Dubu goma ya ciro a aljihunsa ya ajiye mata, ta dinga sa masa albarka, ya mike yace "Ni zan tafi saboda ana jirana bani kadai zan je Zarian ba" Hajja tace "To maza kaje Allah ya tsare, ke Mayraah ai kina nan har gobe ko" Usman yace "Aa tare za mu koma gida yanzu" Hajja tace "Tare kuma? Saurin me take" Usman ya kalli Mayraah yace "Tashi mu je" Mikewa tayi tace "Hajja in sha Allahu zan dawo ni kadai" Hajja dai bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Wato Ammi ce tace kar ki zauna ko??" Usman yace "Ai ke dama kin iya zarge zarge a ranki" Mayraah tace "Bata ce haka ba Hajja, kawai akwai wani aiki da nake yi na makaranta ne" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Badiyya ta fito da akwatunanta uku tana turasu, Hajja ta mike tace "Tafiyar kenan Badiyya?" Ba tare da Badiyya ta kalleta ba tace "Eh" Hajja tace "To ai kawai sai ki bi su Usman su ma gida za su tafi yanzu" Usman yayi saurin cewa "Wani Usman din?" Hajja ta kallesa baki bude, lokaci daya ta hasala tace "Wai me ku ka dau Badiyyar nan ne? Bare ko me? Er kanwar uwarka ce fa uwa daya uba daya, kwata kwata kun dauki tsangwama kun yafa ma yarinya marainiya ba uwa ba uba" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Usman ya fice daga parlon ita dai Mayraah ta kasa motsawa daga inda take, Usman ya leko parlon ganin Mayraah bata biyosa ba yace "Ke me kike jira Malama" Mayraah ta sauke idonta kasa ta nufi kofa, Hajja ta dau dubu gomansa da sauri cikin kuka tana mika masa tace "Gashi bana so ka kara fetur a hanyar Zaria" ko juyawa shi dai bai yi ba har ya fita, Mayraah dai sai bin sa take don bata son yayi mata masifa.....


07087865788

WhatsApp only.

Mayraah Page 4 By Khalesat Haiydar

 

Post a Comment

0 Comments

Ads


Click Here To Download This Book