💖💖 *MAYRAAH*💖💖
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
9.....
Aunty Mariya na kallon Hajja tayi kasa kasa da murya tace "Don girman Allah Hajja in zaki koma gida kice mata ta bi ki ku tafi, kin dai san halin Mama Ladi" Hajja tace "Haba ai kwa bari ko kwana daya tayi ko Mariya, hanya fa ta biyo tun asuba" Aunty Mariya tace "Wllh tana wuce yau a gidan nan ina me tabbatar maki babu inda zata je har sai an gama bikin nan Hajja, ke kadai ce zaki gaya mata taji, kice mata baƙi sun fara yawa a nan kawai ta fito ku tafi gidanki" Hajja tace "Toh amma dai za a bari tayi wanka ta ɗan huta ta ci abinci tukunna ko?" Aunty Mariya tace "Aa dama ai sai ta ci abinci Hajja, ba yanzu nake nufi ba, ba sai in Maheer zai maida ke gida sai ki mata dubara ki tafi da ita" Hajja tace "Toh babu damuwa" Aunty Mariya ta mike ta wuce kitchen don hada ma Mama ladi abinci, mikewa Mayraah tayi ta wuce sama, Hajja na kallon Badiyya dake danna wayarta tace "ke sakko ki karasa zuge akwatin sarkokin nan kada wani abu ya ɓata masu a shiga uku, da ganinsu kasan masu tsada ne, basu yi kama yan kasar nan bane" A takaice Badiyya tace "Ban ga zan iya ba" Hajja ta buda baki tana kallonta, can tace "Toh Allah ya baki hakuri, abinda dai da yatsuna ni ba kuturwa ba, ai ni sai in rufe meye a ciki" Tana fadin haka ta mike tana kokarin rufe akwatin da kyau, Hajja ta ci gaba da cewa "Wani ma ba sai yace hassada kike ma kanwar taki ba, ji fa tun da ake bude kayan nan babu wanda kika yaɓa a ciki balle kice Allah ya sanya alkhairi kema Allah ya dora ki a danshinta, sai wani nukurci da murtuke fuska kike, wannan dai ba yi bane in gaya maki gaskiya, in zaki canza halin ki tun wuri ki canza wllh" Wani fitsararren kallo Badiyya ke ma Hajja kamar zata rufeta da duka, Hajja dai ko damuwa bata yi ba, ta koma ta zauna tana cewa "Dama duk wanda ma zai zo ba sai an sake fito masa da Gwal din ba, ido ba kyau, gwara a fada da baki ace gashi an sa gwal kawai shikenan...." Nan da nan facial impression din Badiyya ya canza jin Hajja ta ambaci gwal, gwal? Wato har da gwal a lefen, Hajja ta ci gaba tana cewa "Gwara a adana sa kawai, kar a sake fitowa da shi, ba a san zuciyar wani ba" Badiyya ta hadiye wani abu da kyar, tana sake bin duk akwatunan da kallo, yanzu har da gold cikin akwatin nan wai? Hajja ta kwalo ma Aunty Mariya kira, Aunty Mariya ta fito daga kitchen tace "Gani Hajja" Hajja tace "Dama cewa nayi kar a kuma fito da gwal din nan a nuna ma kowa don Allah" Aunty Mariya tace "Haba tun ranan da aka kawo kayan ba a sake fitowa da shi ba sai yau da kika zo ai Hajja" Hajja tace "To da kyau, hakan yafi, amma sai nake ga bai ma kamata a bar sa a akwatin ba, wani fa ba don Allah yake zuwa ganin kayan ba sai don ya tafka halin bera" Aunty Mariya tace "Ai ba ciki suke ba dama, na kai sama yana cikin jakata tun ranan, zuwanki ne yasa na fito da shi" Hajja tace "Toh madallah, gwara haka" Juyawa Aunty Mariya tayi ta koma kitchen, Ammi ta sauko downstairs tana kallon Badiyya tace "Badiyya tafi kitchen ki hado ma Mama Ladi shayi, tace shayi da kwai da bread zata ci, akwai full bread a kitchen ba a taɓa ba, sai ki soya mata kwai hudu, Madara da Milo kuma ki kai mata gwangwanin gaba daya, tana nan dakin Mayraah" Badiyya ta mike tace "Toh" Hajja tace "Banda abun Ladi cikin zafin nan me zata yi da shayi kamar shugaban mayu, ga dai tuwo da taushe me kyau anyi nima har na ci" Ammi tace "Gwara dai a kai mata, idan ya so anjima sai a kai tuwon" Badiyya ta nufi kitchen ta sanar ma Aunty Mariya abinda Ammi tace, Aunty Mariya tace "Ita kuma me zata yi da shayi da ranan nan haka?" Badiyya dai bata ce komai ba ta kunna gas zata daura ruwa, Aunty Mariya tace "Toh sai ki soya mata kwai, anjima idan za su tafi sai a zuba mata tuwon a Warmer su tafi da shi" Daga haka ta fice daga kitchen din, Badiyya har ta mance yaushe rabon ta kunna gas, kullum Hajja ce ke masu girki a gida, hatta ruwan zafin nan idan tana bukata yana cikin flask zata tarar Hajja ta cika mata dam, don haka babu hadinta da gas, ta bude fridge ta fiddo kwai hudu ta fasa, ta dau maggi cube biyu ta marmasa a ciki, ta saka gishiri, sai kuma ta dinga kalle kallen kitchen din tana tunanin sai kuma me za a saka a kwan? Ta nufi inda taga Scotch bonnet da albasa ta dau wuka ta fara yanka albasan, da kyar ta gama yankawa don sai hawaye take kamar an buda pampo alamar rashin sabo, ta zuba tarugun manya uku a blender da albasan ta markada su sannan ta juye a kwan ta kada da kyau, tunawa tayi bata sa curry ba tayi maza ta fara duba inda curry yake a kitchen din har ta gani sannan ta zuba a kwan, ta kara beating dinsa, minti biyar ta dauka tana soya kwan, sai da taga kamar konewa yake yi ta maza ta juye a plate, cikin few minutes ta gama hada komai a katon tray sannan ta fito daga kitchen din, Aunty Mariya tace "Sai kace me soya kwai crate daya Badiyya" Badiyya bata ce komai ba ta wuce sama tana murguda baki, tana shiga dakin Mayraah ta tarar da Mama Ladi zaune kasan carpet tana ta mulka Vaseline a jikinta da fuska, sai wani naso take kamar an tsomata a man gyada a fiddo, Mama Ladi tace "Sannu er nan, Allah maki albarka har da kwan aka soyo ko?" Badiyya tace "Ehh bari in dauko gwangwanin Madara da Milon" Mama Ladi ta washe baki tace "To yi maza" Badiyya na fita ba a dau lokaci ba ta dawo ta ajiye ma Mama Ladi gwangwanayen sannan ta zauna gefen gado tana kallonta tace "Wannan Vaseline din da kika lafta fa Mama Ladi?" Mama Ladi tace "To ai ji nayi kamar hunturu kar inje in fara bushewa kamar an tono ni a rami..." Badiyya tayi dariya tace "AC fa aka kunna maki ba wani hunturu ake ba" Mama Ladi tace "Au too, ni dai naji sanyi ba kakkautawa sai nayi zaton hunturu ake a nan" jawo cup tayi ta fara hada shayin, Badiyya ta dawo kusa da ita tayi kasa da murya tace "Mama Ladi kinsan me naji Aunty Mariya na ce ma Hajja?" Mama Ladi ta kalleta da sauri tace "Aa" Badiyya tace "Wllh wai ce ma Hajja tayi don Allah in zata tafi ta tafi dake gidanta su baza su iya da halinki ba gaskiya" A hankali Mama Ladi ta ajiye flask din hannunta tace "Ita Mariyar ce tace haka a kaina?" Badiyya tace "Wallahi, nufinta ke fitinanniya ce baza ki zauna masu a gida ba Hajja ta tattara ki ta tafi dake idan zata koma gida anjima, amma fa bana son ki ce masu komai, kawai dai idan Hajja tace ki tashi ku tafi kice mata a'a ke gidan biki kika zo babu inda za ki" Mama Ladi tayi mitsi mitsi da ido tace "Ka ji shegiyar da naci kashinta na ci fitsarinta, a lokacin fa gashin kanta yanda kika san hammatan ɗan iska ba kyan gani, gashi bata da aiki sai kirba kashi a wando ta bar ni da wanke mata, shine take fadin haka yau a kai na? Ni Mariya take cewa a kora a gidan nan sabida ta auri ɗan gwangwan ya kai ta makka?" Badiyya ta fara zare ido tace "Don Allah ni dai kiyi shiru, sirri na zo na gaya maki fa kina neman aji a waje, sannan na riga na gaya maki amsan da za ki basu idan Hajja tace ki bi ta, shikenan kawai ki bar zancen, don Allah kar ki ce na gaya maki wannan maganar Mama Ladi" Mama Ladi ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Sai kace wata yarinya zan ce ga abinda kika gaya min, ki tafi kawai ki hada min shayin, madaran cokali shidda zaki zuba min haka nake sha a gida" Badiyya ta hada mata shayin ta ajiye a gabanta, Mama Ladi ta yanko kwai ta kai baki, tana fara taunawa ta maza ta tofar kan farantin tana yamutsa fuska a gigice tace "Wani azzalumin ne ya min suyan kwan nan?" Badiyya tayi tsuru tsuru tana kallonta, Mama Ladi ta mike tace "Na shiga uku na lalace, Badiyya wace shegiyar ce ta soya min kwan nan a gidan nan?" Badiyya ta ɗan daure fuska tace "Me ya samu kwan ne wai?" Mama Ladi tace "Ki ɗan dana ki ji mana er nan, ga uban gishiri ga yaji, wacece tayi min wannan aika aikan, ko dai Mariyar ce?" Badiyya ta ɗan tabe baki tace "Me aikin gidan ce" Mama ladi tace "Mu je ki nuna min ita, to ko dai Mariyar ce ta sa ta tayi min wannan walakancin?" Badiyya ta zaro ido tace "Na shiga uku, don girman Allah ki rufa min asiri Mama Ladi, kar fa kije kice masu ga abinda nace in shiga uku, ke ba a sirri dake ne?" Mama Ladi tace "Yo ni ina ruwana da abinda kika zo kika gaya min, ki ɗan dana kwan nan kiji don Allah" Ammi ce ta shigo dakin tace "Kin idar Mama Ladi" Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Ammi taho ki ga abinda mai aikinki ta soyo ta kawo min saboda ta ga ni ba er birni bace, amma abinda bata sani ba nima ai a birnin aka haifeni" da mamaki Ammi tace "Me aiki kuma, Badiyya ce fa na sa ta hado maki shayin ta soya kwan Hajja" Mama Ladi ta juya tana kallon Badiyya da mamaki, Badiyya ta wani dauke kanta, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ke a haka kike son ki kwace ma yarinya saurayi ko girki baki iya ba goɗe goɗe da ke? Idan ba mantawa nayi fa da shekara biyu ko daya Mashir ya girme ki, amma ace guzuma irinki baki iya sarrafa kwai ba, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to kinyi ma kwai wannan azababben suyan ina ga idan girki za ki yi me gaba daya? Aa Hajja ta cuce ki, me za ayi da mace da bata iya girki ba sai kwalliya a fuska a wannan zamanin, shi saurayin Meran me zai yi da warce bata iya girki ba?" Ammi dai na tsaye ta kasa cewa komai, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Wallahi baki ji kwan ba kamar ba kwai ba Ammi, ni na zata flawa ce aka lafta ma tarugu da maggi da gishiri, ko sati biyu fa ba ayi ba matar nan taje har karaye ta sameni tana kuka wiwi wai Mera ta kwace mata saurayi gashi har za ayi aure kuma babu wanda ya dau mataki a kai kowa ya goyi bayan Mera, wllh ina ta tausayinta nace amma kun ci amanar Rukayya, kuma idan baku yi hankali ba sai wuta ta ci ku, har na kullaci Meran dazu tana gaisheni nayi mata banza ashe masharanciya ce Badiyya ban sani ba, nasan da Mera aka saka wannan suyan da tuni na kusa cinyewa ina neman kari, aa gaskiya Hajja ta cuci Badiyya, kuma nayi da na sanin goya mata baya da nayi da taje wajena" Mikewa Badiyya tayi ta nufi kofa fuuuu ta fice daga dakin kamar zata tashi sama, Mama Ladi tace "Muguwa kawai, Mijin Mera sai gani sai hange tunda ke makaryaciya ce warce bata iya girki ba" Ammi dai ta rasa ma me zata ce, wato karya Badiyya ta musu ta tafi bichi ashe Karaye ta tafi wajen Mama Ladi, Mama Ladi ta koma ta zauna tace "Gaskiya a fitar min da wannan azaban a kira Mera ta soya min kwan da zan iya ci" Ammi ta sunkuya ta dau plate din kwan tace "Kiyi hakuri Mama Ladi, yanzu za a kawo maki wani" Mama Ladi tace "Hakuri ai ya zama dole, munafukar yarinya wai Mera ta kwace mata saurayi, wani saurayin arziki ne zai aureta bata iya girki ba, wanda bai iya soya kwai ba ai babu abinda zai iya kuma a rayuwarsa har ya mutu" Ammi dai ta fita daga dakin. Bayan la'asar Hajja ta tafi sama har zuwa dakin Mayraah wajen Mama Ladi, Rabon Hajja da haurawa saman gidan zai yi shekara bakwai, tun wani rashin lafiya da Ammi tayi, Hajja na tsaye bakin kofa bayan ta shiga dakin tace "Ke Ladi tashi zaki yi tunda kin huta mu tafi gidana don nan baƙi yawa za su yi zuwa nan da kwanaki kadan, gwara mu je inda zaki sake babu takura" Mama Ladi dake kishingide jikin pillow tana sakace hakora bayan ta ci kaza tayi nak tace "Ko yaya?" Hajja tace "Kwarai kuwa, kinga ni ma gida zan tafi Maheer zai ajiye ni yanzu" Mama Ladi tace "Toh shikenan, a kira min Mariya ta zo ta dau min akwatina mu sauka kasa akwai dukiyana a ciki bazan ba yara ba gaskiya" Hajja tace "Toh bari in mata magana" Hajja ta juya ta fita, bayan wani lokaci sai ga ta ta dawo tare da Aunty Mariya, Hajja tace "Akwatinta zaki dauka a saka mata a mota za mu tafi gida" Aunty Mariya ta shigo dakin da sauri ta nufi inda akwatin yake ta duka zata dauka Mama Ladi tace "Munafuka algunguma wato daukar akwatin zaki yi, to babu inda zanje ina nan tunda ba gidanki bane balle na mijinki, har zaki je ki wani ce ma Hajja ta lallabani ta tafi da ni tunda gani barbadaddiya, to ina nan har sai an gama biki tunda ba wajen Hajja na zo ba, ke har kin manta irin azabar da kika min kina yarinya da zaki dinga kakkabi da ni? To wallahi babu inda zan je, ai ba gidanki na zo ba, babu wanda ya isa ya hanani zama gidan nan har sai bayan biki" Aunty Mariya was sooo shock, don kasa motsawa tayi a inda ta duƙa, Hajja tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wani irin magana kike Ladi, a ina kika ji wannan maganar haka?" Mama Ladi tace "Badiyya ce ta zo nan ta gaya min, kuma wllh bazata maku sharri ba ji tayi an fada ne, in dai an ga na bar gidan nan to Mamuda ne ya koreni, amma ita kanta Ammin tayi kadan Al-qur'an, ai bikin jikokina biyu na zo Mera da Mashir" Tana kai wa nan ta juya masu baya ta ci gaba da kwanciyarta, Hajja dai ta kasa cewa komai balle Aunty Mariya da ta kasa dagowa kamar kasa ya bude ta shige, Ammi da ke kokarin shigowa dakin dama a kan kunnenta aka yi komai, ta juya sum sum sum ta bar wajen ba tare da ta bari an ma san tana wajen ba.... Hajja na saukowa parlor ta dau er jakarta tace "To da Alkhairi na tafi gida ni kam" Ammi dai na zaune kan kujera banda dariya babu abinda take, sai ga Aunty Mariya ta sauko kasa kamar wanda ruwa ya cinye tace "Wallahi wallahi sai na yi ma Badiyya abinda bata taɓa tunani ba, ba tace ita magulmaciya bace munafuka, Ni zata je ta hada da wannan matar?" Hajja tace "A dai dinga tunawa marainiya ce" Daga haka ta bar masu parlon, Nan Aunty Mariya ta hau shiga dakunan gidan ranta a bace tana neman Badiyya, Sabira tace "Ai Aunty Badiyya ta bar gidan nan tun dazu fa Hajiya"
Musharraf yayi parking kofar gidansu wajen karfe shidda na yamma zai shiga ya gaida Mami don bai da intention din kwana a gidan ranan, throughout today wayarsa a flight mode ya bar sa yasan Mami ta nemesa har ta gaji, balle kuma Mayraah, duk yau ita ma basu yi magana ba, yanzun ma da ya taho gida ba kunna wayar yayi ba still, kawai baya son Mami ta daga hankalinta ne, Yana sauka motar ya nufi gate din gidan, ya amsa gaisuwan da Mai gadi ke masa without looking at him, zai shiga ciki Mai gadin yayi kasa da kai cike da ladabi yana biye da shi yace "Yallabai an samu akasi fa" Musharraf ya juyo da sauri yana kallonsa yace "Akasin me?" Mai gadi yayi kasa da murya kamar munafuki yace "Wallahi dazu Hajiya za su fita da Dreba sai ga dai wannan mutumin da ya kawo takardan nan wancan ranan...." Musharraf ya katsesa a rikice yace "Sai me ya faru??" Mai gadin da har ya tsorata ya fara kame kame, a fusace Musharraf yace "Malam ka gaya min ya aka yi??" Mai gadin yace "Wallahi a kan idonta mutumin ya bani irin wannan takardan na ranan nan, don dreba ya fito da motar kenan daga cikin gidan za su tafi... Shine Hajiya ta sauke gilashin mota ta amshi takardan a hannuna, kaga ai bazan ce mata a'a ba ranka shi dade" Musharraf da yaji wani zufa na keto masa yace "Ita da waye a motar??" Mai gadin yace "Aa ita kadai ce, ina jin Check up zata je" Musharraf bai sake sauraronsa ba ya shige cikin gidan da sauri, cikin few seconds sai ga shi a parlor, babu kowa a parlon ya haura zuwa bangaren Mami, a parlonta ya sameta da mai aikinta dake shiga tayata hira a kai a kai, Mai aikin ta mike ganin Musharraf ta gaishesa da ladabi sannan tayi ma Mami sallama ta fita, Musharraf yayi kokarin calming kansa down yana kallon Mami dake kallonsa ita ma, A hankali yace "Good evening Ma" Mami ta sauke idonta daga kallonsa tace "Evening, me yasa ka kashe waya tun safe?" Ya zauna saman kujera zuciyarsa bai daina bugawa ba yace "Ina hutawa ne yau" Mami tace "Okay" Daga haka ta mike ya bi ta da kallo gabansa na mugun bugawa, bedroom dinta ta shiga sai ga ta ta dawo rike da Envelope a hannunta tana kallonsa, kadan ya rage Musharraf bai samu heart attack ba a lokacin, don sai da yaji komai nasa ya tsaya for some seconds....
A gigice Aunty Mariya ta shigo dakin Ammi tana kallonta tace "Ammi dama baƙi na shiga dakin Usman ne?" Ammi da lokaci daya hankalinta ya tashi ganin yanayin kanwar tata ta mike tace "Me ya faru Mariya?" Aunty Mariya da zufa ke karyo mata tace "Kinsan a dakinsa na ajiye jakata da akwatina tun ran da na zo..." Ammi tace "To me ya faru? Ai babu wanda yake shiga dakinsa a gidan nan sai Maheer shima ba ko da yaushe ba" Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku Ammi ban ga zinarin akwatin lefen Mayraah da na saka a handbag dina ba na kai dakin dazu bayan da aka nuna ma Hajja" Sosai gaban Ammi ma ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Mariya ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna gefen gado tace "Yanzun nan na shiga dakin zan dau kudi a jakar naga babu kudin, kusan dubu talatin, nan na duba inda na ajiye zinarin da sauri, naga wayam babu an dauke har shi" Tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai, Ammi tsabar confusion ta kasa cewa komai, Aunty Mariya ta mike ta fice daga dakin tana kuka tace "Waye ya mana wannan aika aikan...."
*Start making ur payment before the end of free pages fans, kar a ji ni shiruuuu*
07087865788✍🏻
WhatsApp only
0 Comments